Pular para o conteúdo
Publicidade

Karin Magana 5

8 Ku yi nesa da hanyarta,

kana ku je kusa da ƙofar gidanta,

9 don kada ku ba da ƙarfi mafi kyau ga waɗansu

da kuma shekarunku ga wani marar imani,

10 don kada baƙi su yi biki a kan dukiyarku

wahalarku ta azurta gidan wani mutum dabam.

11 A ƙarshen rayuwarku za ku yi ta nishi,

sa’ad da namanku da jikinku suka zagwanye.

12 Za ku ce, "Me ya sa na ƙi horo!

Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!

13 Ban yi biyayya da malamaina ba

ko in saurari masu koyar da ni.

14 Na zo gab da hallaka gaba ɗaya

a tsakiyar dukan taron."

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também