Pular para o conteúdo
Publicidade

Karin Magana 6

6 Ku tafi wurin kyashi, ku ragwaye;

ku lura da hanyoyinsa ku zama masu hikima!

7 Ba shi da jagora

ba shugaba ko mai mulki,

8 duk da haka yakan yi tanade-tanadensa da rani

ya kuma tattara abincinsa a lokacin girbi.

9 Har yaushe za ku kwanta a can, ku ragwaye?

Yaushe za ku farka daga barcinku?

10 Ɗan barci, ɗan gyangyaɗi,

ɗan naɗin hannuwa don a huta,

11 talauci kuwa zai zo kamar yan hari

rashi kuma kamar ɗan fashi.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.

Veja também