19 Kada ku yi ramuwa, abokaina, sai dai ku bar wa Allah. Gama a rubuce yake cewa, "Ramuwa tawa ce; zan kuwa sāka,"12.19 M Sh 32.35 in ji Ubangiji. 20 A maimakon haka,
"In abokin gābanka yana jin yunwa, ka ciyar da shi;
in yana jin ƙishirwa, ka ba shi ruwan sha.
Ta yin haka, za ka tara garwashin wuta a kansa."12.20 K Mag 25.21,22
21 Kada ku bar mugunta ta sha kanku, sai dai ku sha kan mugunta ta wurin aikata nagarta.