11 Gama alherin Allah mai kawo ceto ya bayyana ga dukan mutane. 12 Yana koya mana mu ce, "A’a" ga rashin tsoron Allah da kuma sha’awace-sha’awacen duniya, mu kuma yi rayuwa ta kamunkai, ta adalci da kuma ta tsoron Allah a cikin wannan zamani, 13 yayinda muke sauraron begenmu mai albarka bayyanuwar ɗaukakar Allahnmu mai girma da kuma Mai Cetonmu, Yesu Kiristi,