Publicidade

Aprender

Por Bíblia Online

Aprender é vocação do discípulo. Jesus disse: aprendei de mim. A Bíblia convida a aprender com humildade, perseverança e disposição — sentados aos pés do Mestre.

Aprender de Jesus

Tomai sobre vós o meu jugo e aprendei de mim. O Espírito Santo nos ensinará todas as coisas e nos recordará tudo.

Ku ɗauki karkiyata a kanku, ku kuma yi koyi da ni, gama ni mai tawali’u ne marar girman kai, za ku kuwa sami hutu don rayukanku. Gama karkiyata mai sauƙi ce, kayana kuma marasa nauyi ne."

Saboda haka ku tafi, ku mai da dukan al’umman duniya su zama almajiraina, kuna yi musu baftisma a cikin da Gal 3.27 sunan Uba, da na Ɗa, da na Ruhu Mai Tsarki, kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani."

Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko cikin sunana, zai koya muku kome, zai kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku.

Yesu ya amsa ya ce, "Koyarwata ba tawa ba ce, ta fito ne daga wurin wanda ya aiko ni.

Game da ku kuwa, shafan nan da kuka karɓa daga gare shi tana nan a cikinku, ba kwa kuma bukata wani koyar da ku. Amma kamar yadda shafan nan tasa tana koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.

Ensino e sabedoria

O temor do Senhor é o princípio do saber. A disciplina do Senhor forma o caráter e abre caminhos de entendimento.

Tsoron Ubangiji shi ne masomin ilimi,

amma wawaye sun rena hikima da horo.

Ɗana, kada ka rena horon Ubangiji

kada kuma ka ƙi tsawatawarsa,

domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,

kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.

Na bishe ka a hanyar hikima

na kuma jagorance ka a miƙaƙƙun hanyoyi.

Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani,

amma duk mai ƙin gyara wawa ne.

Sai ku sani fa a cikin zuciyarku cewa kamar yadda mutum kan horar da ɗansa, haka Ubangiji Allahnku ke horar da ku.

Comunidade de aprendizado

Ensinem e aconselhem-se mutuamente. A igreja é escola de Cristo — onde todos ensinam e todos aprendem juntos.

Ku bar maganar Kiristi ta zauna a cikinku a yalwace yayinda kuke koya, kuna kuma yi wa juna gargaɗi da dukan hikima, da kuma yayinda kuke waƙoƙin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya tare da godiya a zukatanku ga Allah.

Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.

Kowace rana, a filin haikali da kuma gida-gida, ba su fasa koyarwa da kuma shelar labari mai daɗi cewa Yesu shi ne Kiristi ba.

Kun san cewa ban yi wata-wata yin muku wa’azi game da duk abin da zai amfane ku ba amma na koyar da ku a fili da kuma gida-gida.

Duk abin da kuka koya ko kuka karɓa ko kuka ji daga wurina, ko kuka gani a cikina, ku yi aiki da shi. Allah na salama kuma zai kasance tare da ku.

Abin da ya kamata a koyarwa wa ƙungiyoyi dabam-dabam

Dole ka koyar da abin da yake bisa sahihiyar koyarwa.

Ouvir e praticar

Ensina-me a fazer a tua vontade. Guia-me pela tua verdade. O verdadeiro aprendiz pratica o que ouviu do Mestre.

Ka koya mini in yi nufinka,

gama kai ne Allahna;

bari nagarin Ruhunka

bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa.

Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji,

ka koya mini hanyoyinka;

ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini,

gama kai ne Allah Mai cetona,

kuma begena yana a kanka dukan yini.

Ubangiji nagari da mai adalci ne;

saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.

Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai

ya kuma koyar da su hanyoyinsa.

Zan umarce ka in kuma koyar da kai a hanyar da za ka bi;

Zan ba ka shawara in kuma lura da kai.

Raina yana marmarinka da dare;

da safe kuma raina yana son ganinka.

Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya,

mutanen duniya kan koyi adalci.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-