Buscar a Deus
Buscar a Deus é o chamado mais urgente da Bíblia. Buscai primeiro o Reino de Deus. Os que buscam de todo coração encontram — porque Ele se deixa encontrar pelos que o procuram.
Buscai ao Senhor
Buscai ao Senhor enquanto se pode achar. Buscai e achareis. O Senhor recompensa os que o buscam com diligência.
Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;
ku yi kira gare shi tun yana kusa.
Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa;
ku yi kira gare shi tun yana kusa.
Hukunci da kuma ceto
"Na bayyana kaina ga waɗanda ba su tambaye ni ba;
ina samuwa ga waɗanda ba su neme ni ba.
Ga al’ummar da ba tă kira bisa sunana ba,
Na ce, ‘Ga ni, ga ni.’
Yakan ba da ƙarfi ga waɗanda suka gaji
yă kuma ƙara ƙarfi ga marasa ƙarfi.
Ko matasa ma kan gaji su kuma kasala,
samari kuma kan yi tuntuɓe su fāɗi;
amma waɗanda suka dogara ga Ubangiji
za su sabunta ƙarfinsu.
Za su yi firiya da fikafikai kamar gaggafa;
za su kuma yi gudu ba kuwa za su gaji ba,
za su yi tafiya ba kuwa za su kasala ba.
Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
Ku dogara ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
"Kai kuma ɗana Solomon, ka san Allah na mahaifinka, ka kuma yi masa hidima da dukan zuciya da kuma yardar rai, gama Ubangiji yana binciken zuciya, yana kuma gane dukan aniyar tunani. In ka neme shi, za ka same shi; amma in ka yashe shi, zai ƙi ka har abada.
in mutanena, waɗanda ake kira da sunana, sun ƙasƙantar da kansu, suka kuma yi addu’a, suka nemi fuskata, suka kuma juye daga mugayen hanyoyinsu, zan ji daga sama in kuma gafarta zunubinsu in kuwa warkar da ƙasarsu.
Ya fita ya je ya sadu da Asa ya kuma faɗa masa, "Ka saurare ni, Asa da kuma dukan Yahuda da Benyamin. Ubangiji yana tare da ku sa’ad da kuke tare da shi. In kuka neme shi, za ku same shi, amma in kuka yashe shi, zai yashe ku.
Sauye-sauyen Asa
Sai Ruhun Allah ya sauko a kan Azariya ɗan Oded. Ya fita ya je ya sadu da Asa ya kuma faɗa masa, "Ka saurare ni, Asa da kuma dukan Yahuda da Benyamin. Ubangiji yana tare da ku sa’ad da kuke tare da shi. In kuka neme shi, za ku same shi, amma in kuka yashe shi, zai yashe ku. Tun da daɗewa Isra’ila ba su da Allah na gaskiya, babu firist da zai koyar, kuma babu doka. Amma cikin wahalarsu suka juya ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, suka kuma neme shi, suka kuwa same shi. A waɗancan kwanaki akwai hatsari a yin tafiye-tafiye, gama dukan mazaunan ƙasashe suna cikin babbar damuwa. Wata ƙasa takan murƙushe wata, wani birni kuma yakan murƙushe wani, domin Allah ya wahalshe su da kowace irin damuwa. Amma game da ku, ku ƙarfafa kada ku fid da zuciya, gama za a ba ku ladan aikinku."
Sa’ad da Asa ya ji waɗannan kalmomin da annabcin Azariya ɗan Oded annabi ya faɗa, sai ya sami ƙarfi hali. Ya kawar da gumaka masu banƙyama daga dukan ƙasar Yahuda da Benyamin da kuma daga garuruwan da ya ci da yaƙi a ƙasar tudu ta Efraim. Ya gyaggyara bagaden Ubangiji da yake a gaban shirayin haikalin Ubangiji.
Sa’an nan ya tattara dukan Yahuda da Benyamin da kuma mutane daga Efraim, Manasse da Simeyon waɗanda suke zaune a cikinsu, gama jama’a mai girma ta zo wurinsa daga Isra’ila sa’ad da suka ga cewa Ubangiji Allahnsa yana tare da shi.
Suka taru a Urushalima a wata na uku na shekara ta goma sha biyar ta mulkin Asa. A lokacin suka miƙa hadaya bijimai ɗari bakwai da tumaki da kuma awaki dubu bakwai ga Ubangiji daga ganimar da suka dawo da ita. Suka yi alkawari don su nemi Ubangiji Allah na kakanninsu, da dukan zuciyarsu da kuma dukan ransu. Aka kashe dukan waɗanda ba su nemi Ubangiji, Allah na Isra’ila ba, ko ƙarami ko babba, namiji ko ta mace. Suka yi rantsuwa ga Ubangiji da babbar murya, da ihu da garayu da ƙahoni. Dukan Yahuda suka yi farin ciki game da rantsuwar domin sun yi rantsuwar gabagadi. Suka nemi Allah da gaske, suka kuma same shi. Saboda haka Ubangiji ya ba su hutu a kowane gefe.
Sarki Asa ya tuɓe mahaifiyar mahaifiyarsa daga matsayinta na mahaifiyar sarauniya, domin ta gina ginshiƙin banƙyama na Ashera. Asa ya rurrushe shi, ya farfasa shi ya kuma ƙone shi a Kwarin Kidron. Ko da yake bai kawar da masujadan kan tudu daga Isra’ila ba, zuciyar Asa ta cika da bin Ubangiji dukan kwanakinsa. Ya kawo azurfa da zinariya da kayayyaki a haikalin Allah waɗanda shi da mahaifinsa suka keɓe.
Ba a ƙara yin yaƙi ba sai a shekara ta talatin da biyar ta mulkin Asa.
De todo o coração
Buscar-me-eis e me achareis quando me buscardes de todo o coração. O Senhor é bom para os que o buscam.
Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.
Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.
"Maganata ba wuta ba ce," in ji Ubangiji, "kuma kamar gudumar da kan ragargaza dutse?
Amma daga can in kuka nemi Ubangiji Allahnku, da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, za ku same shi.
Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa
suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
Albarka ta tabbata ga waɗanda suke kiyaye ƙa’idodinsa
suke kuma nemansa da dukan zuciyarsu.
Na neme ka da dukan zuciyata;
kada ka bar ni in kauce daga umarnanka.
Raina ya gaji da baƙin ciki;
ka ƙarfafa ni bisa ga maganarka.
Zan yi ta yawo a sake
gama na nemi farillanka.
Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
Ku sa rai ga Ubangiji da kuma ƙarfinsa;
ku nemi fuskarsa kullum.
Zuciyata kan faɗa game da kai, "Nemi fuskarsa!"
Fuskarka, Ubangiji, zan nema.
Ya Allah, kai ne Allahna,
da nacewa na neme ka;
raina yana ƙishinka,
jikina yana marmarinka,
cikin busasshiyar ƙasar da ta zozaye
inda babu ruwa.
Buscar e encontrar
Pedi e dar-se-vos-á. O Senhor está perto de todos os que o invocam em verdade. Quem o busca não ficará insatisfeito.
Roƙa, nema, ƙwanƙwasa
"Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.
"Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa. Gama duk wanda ya roƙa, yana karɓa, mai nema yana samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma, za a buɗe masa ƙofa.
"Don haka ina faɗa muku, ku roƙa, za a ba ku, ku nema za ku samu, ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.
Amma ku nemi mulkinsa, za a kuwa ƙara muku waɗannan abubuwa.
Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma."
Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,
gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.
Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini;
ya cece ni daga dukan tsoro.
Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa,
amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.
Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji
zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
Ubangiji ya duba daga sama
a kan ’yan adam
don yă ga ko akwai wani da ya gane,
wani wanda yake neman Allah.
Ya Ubangiji, ka bincike ni
ka kuwa san ni.
Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi;
ka san tunanina daga nesa.
Zai sami albarka daga Ubangiji
da fiffitawa daga Allah Mai cetonsa.
Irin tsaran waɗanda suke nemansa ke nan,
waɗanda suke neman fuskarka, ya Allah na Yaƙub. Sela
Força na busca
Buscai o bem e não o mal. Sede fortalecidos no Senhor. A busca por Deus traz renovação e plenitude de vida.
Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila.
"Ku neme ni ku rayu;
Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila.
"Ku neme ni ku rayu;
Ku yi nagarta, ba mugunta ba;
don ku rayu
sa’an nan Ubangiji Allah Maɗaukaki zai kasance da ku,
kamar yadda kuka ce zai yi.
Ina addu’a cewa daga yalwar ɗaukakarsa zai ƙarfafa ku da iko daga ciki ta wurin Ruhunsa.
Kayan yaƙi na Allah
A ƙarshe, bari ƙarfin ikon Ubangiji yă ba ku ƙarfi.
Allah yă ƙarfafa ku da dukan iko bisa ga ɗaukakar ƙarfinsa domin ku kasance da jimrewa sosai da kuma haƙuri, cikin farin ciki
Gama Allah bai ba mu ruhun tsoro ba, sai dai ruhun iko, na ƙauna da kuma na kamunkai.
In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.
In ba tare da bangaskiya ba kuwa, ba ya yiwuwa a gamshi Allah, domin duk mai zuwa wurin Allah dole yă gaskata cewa yana nan, kuma shi ne yakan sāka wa waɗanda suke nemansa da gaske.
Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya."
Bari Ubangiji yă sāka maka saboda abin da ka yi. Bari Ubangiji, Allah na Isra’ila yă sāka maka a yalwace, a ƙarƙashin fikafikan da ka sami mafaka."
Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko masa da ƙarfi, ya sa ya yaga zakin kashi biyu da hannu kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Sai dai bai gaya wa iyayensa abin da ya yi ba.
Sa’an nan Samson ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, "Ya Ubangiji Mai Iko Duka, ya Allah ka tuna da ni, ka ƙarfafa ni sau ɗaya nan kaɗai, ka bar ni da bugu ɗaya kawai in ɗauki fansa a kan Filistiyawa domin idanuna."
Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga mutum.
Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji
da in dogara ga sarakuna.
Duk wanda ya sami mace ya sami abu mai kyau
ya kuma sami tagomashi daga Ubangiji.
Ka kuma san cewa hikima tana da zaƙi ga rai;
in ka same ta, akwai sa zuciya ta nan gaba dominka,
kuma sa zuciyarka ba za tă zama a banza ba.