Pular para o conteúdo
Publicidade

Salmos 14

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda.

1 Wawaye sukan ce a ransu,

"Ba Allah."

Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne;

babu wani da yake yi abu mai kyau.

2 Ubangiji ya duba daga sama

a kan yan adam

don ga ko akwai wani da ya gane,

wani wanda yake neman Allah.

3 Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu;

babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau,

ba ko ɗaya.

4 Masu aikata mugunta za su taɓa koyo.

Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa

kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji?

5 Ga su, tsoro ya sha kansu,

gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai.

6 Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta zama banza,

amma Ubangiji ne mafakansu.

7 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana!

Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa,

bari Yaƙub yi farin ciki Isra’ila kuma yi murna!

Veja também