Publicidade

Céu

Por Bíblia Online

O céu é a morada eterna de Deus e a esperança final do cristão. A Bíblia descreve o céu como lugar de glória, alegria e comunhão perfeita com o Criador.

A morada de Deus

Na casa de meu Pai há muitas moradas. Os céus declaram a glória de Deus — e um dia habitaremos lá eternamente.

A cikin gidan Ubana akwai wurin zama da yawa; da a ce ba haka ba ne, da na gaya muku. Za ni can don in shirya muku wuri.

Sammai suna shelar ɗaukakar Allah;

sararin sama suna furta aikin hannuwansa.

Kowace rana tana yin jawabi;

kowane dare yana nuna sani.

A ɗaukaka ka, ya Allah, a bisa sammai,

bari kuma ɗaukakarka ta kasance a bisa dukan duniya.

Taimakonmu yana a sunan Ubangiji,

Wanda ya yi sama da ƙasa.

Wa nake da shi a sama in ba kai ba?

Ba na kuma sha’awar kome a duniya in ban da kai.

Masomi

A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.

shi da ya gina kyakkyawar fadarsa a cikin sammai

ya kuma kafa harsashenta a duniya,

shi da yakan kira ruwan teku

kuma kwarara su a bisa duniya,

Ubangiji ne sunansa.

Akwai wanda zai iya ɓuya a lungu har da ba zan iya ganinsa ba?"

In ji Ubangiji

"Ban cika sama da ƙasa ba?"

In ji Ubangiji.

"A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka.

Cidadania celestial

A nossa cidadania está nos céus. Ajuntai tesouros no céu, não na terra. O céu é a pátria do cristão.

Amma mu yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi,

Ajiya a sama

"Kada ku yi wa kanku ajiyar dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda kuma ɓarayi sukan fasa, su yi sata. Amma ku yi wa kanku ajiyar dukiya a sama, inda ba tsatsa da asu da za su ɓata su, inda kuma ba ɓarayin da za su fasa, su yi sata.

Yesu ya ce, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne."

Yesu ya amsa ya ce, "In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni."

Sama da ƙasa za su shuɗe, amma maganata ba za taɓa shuɗe ba.

Ku sa hankulanku a kan abubuwan sama, ba kan abubuwan duniya ba.

Esperança eterna

Seremos arrebatados para encontrar o Senhor nos ares. Ainda não se manifestou o que havemos de ser — mas seremos semelhantes a Ele.

Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada.

Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.

Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

Tashi zuwa sama

Bayan ya kai su waje kusa da Betani, sai ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka. Yana cikin sa musu albarka, sai ya rabu da su. Aka ɗauke shi zuwa cikin sama.

Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.

Gama ba da mutane da suke nama da jini ne muke yaƙi ba. Muna yaƙi ne da ikoki, da hukumomi, da masu mulkin duhu, da kuma a ikokin da suke cikin a sararin sama.

Gama ba mu zo duniya da kome ba, ba kuwa za mu fita daga cikinta da kome ba. In dai muna da abinci da sutura, ai, sai mu gamsu da su.

"Kamar yadda sammai suke can nesa da ƙasa,

haka yadda nake yin abubuwa suke dabam da yadda kuke yin abubuwa

tunanina kuma dabam da naku.

Lokaci domin kowane abu

Akwai lokaci domin kowane abu,

da kuma lokaci domin kowane aiki a duniya.

Tsirara mutum yakan fito daga cikin mahaifiyarsa,

kuma kamar yadda ya fito, haka zai koma.

Ba ya ɗaukan kome daga wahalarsa

da zai riƙe a hannunsa.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-