Pular para o conteúdo
Publicidade

Confiar no Senhor

Por Bíblia Online

Confiar no Senhor é a base de toda vida espiritual. A confiança em Deus nos livra do medo, nos dá paz e nos posiciona para receber as promessas divinas.

Confiar de todo coração

Confia no Senhor de todo o coração. Não te apoies em teu próprio entendimento — em todos os caminhos o reconheça.

Ka dogara ga Ubangiji da dukan zuciyarka

kada kuma ka dangana ga ganewarka;

cikin dukan hanyoyinka ka amince da shi,

zai kuwa sa hanyoyinka su miƙe.

Shi wanda yake zama a wurin Mafi Ɗaukaka

zai huta a cikin inuwar Maɗaukaki.

Zan ce game da Ubangiji, "Shi ne mafakata da kagarata,

Allahna, wanda nake dogara."

Tabbatacce zai cece ka

daga tarkon mai farauta

da kuma daga cututtuka masu kisa.

Zai rufe ka da fikafikansa,

a ƙarƙashin fikafikansa kuwa za ka sami mafaka;

amincinsa zai zama maka garkuwa da katanga.

Waɗanda suke dogara ga Ubangiji suna kama da Dutsen Sihiyona,

wanda ba ya jijjiguwa amma dawwammame ne har abada.

Kamar duwatsun da sun kewaye Urushalima,

haka Ubangiji ya kewaye mutanensa

yanzu da har abada kuma.

Ba zai ji tsoron labari marar daɗi ba;

zuciyarsa tsayayyiya ce, tana dogara ga Ubangiji.

Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri;

yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.

Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji

zai kuwa biya bukatun zuciyarka.

Ka sa kanka a hanyar Ubangiji;

ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.

Zai sa adalcinka haskaka kamar hasken safiya,

gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.

Waɗanda suka san sunanka za su dogara da kai,

gama kai, Ubangiji, ba ka taɓa yashe waɗanda suke nemanka ba.

Segurança em Deus

Bem-aventurado o homem que confia no Senhor. Ele é como árvore plantada junto às águas — não temerá quando vier o calor.

"Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,

wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.

Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa

wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.

Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;

ganyayensa kullum kore suke.

Ba shi da damuwa a shekarar fări

ba ya taɓa fasa ba da ya’ya."

Ku dogara ga Ubangiji,

gama shi Ubangiji, ne madawwamin Dutse.

Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;

zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.

Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;

ya zama mai cetona."

Ya Ubangiji Maɗaukaki,

mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.

Waɗansu sun dogara a kekunan yaƙi waɗansu kuma a dawakai,

amma mu, mun dogara a cikin sunan Ubangiji Allahnmu.

Za a durƙusar da su, su kuma fāɗi,

amma mu za mu tashi mu tsaya daram.

Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

da in dogara ga mutum.

Ya fi kyau in nemi mafaka a wurin Ubangiji

da in dogara ga sarakuna.

Não confiar no homem

Não temas — em ti confiarei. Melhor é confiar no Senhor do que confiar no homem ou nos príncipes.

Ga Allah, wanda nake yabon maganarsa,

ga Ubangiji, wanda nake yabon maganarsa,

ga Allah na dogara; ba zan ji tsoro ba.

Me mutum zai iya yi mini?

Amma na dogara a kan ƙaunarka marar ƙarewa;

zuciyata tana farin ciki a cikin cetonka.

Amma na dogara gare ka, ya Ubangiji;

na ce, "Kai ne Allahna."

Mai albarka ne mutumin

da ya mai da Ubangiji abin dogararsa,

wanda ba ya kula da masu girman kai,

waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.

Yesu ya ta’azantar da almajiransa

"Kada zuciyarku ta ɓaci. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni.

Seja o primeiro