Pular para o conteúdo
Publicidade

Salmos 84

Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga gittit.84.0 Kan magana, mai yiwuwa wata kalmar waƙa ce. Na Ya’yan Kora maza. Zabura ce.

1 Ina misalin kyan wurin zamanka,

Ya Ubangiji Maɗaukaki!

2 Raina yana marmari, har yana suma,

don filayen gidan Ubangiji;

zuciyata da namana na da murya

domin Allah mai rai.

3 Har tsada ma ta sami gida,

tsatsewa kuma ta yi wa kanta sheƙa,

inda za ƙyanƙyashe ya’yanta,

wuri kusa da bagadenka,

Ya Ubangiji Maɗaukaki, Sarkina da kuma Allahna.

4 Masu albarka ne waɗanda suke zama a gidanka;

kullum suna ta yabonka. Sela

5 Masu albarka ne waɗanda ƙarfinsu yana daga gare ka,

waɗanda suka kafa zukatansu a yin tafiya zuwa wuri mai tsarki ne.

6 Yayinda suke wuce ta Kwarin Baka,

sukan mai da shi wurin maɓulɓulai;

ruwan sama na farko kuma kan rufe shi da tafkuna.

7 Suna ta ƙara ƙarfi,

har sai kowanne ya bayyana a gaban Allah a Sihiyona.

8 Ka ji addu’ata, ya Ubangiji Allah Maɗaukaki;

ka saurare ni, ya Allah na Yaƙub. Sela

9 Ka dubi garkuwarmu, ya Allah;

ka duba da alheri a kan shafaffenka.

10 Rana guda a filayen gidan sun fi

dubu a wani wuri dabam;

zan gwammaci in zama mai tsaron ƙofa a gidan Allahna

da in zauna a tentunan mugaye.

11 Gama Ubangiji Allah rana ne da kuma garkuwa;

Ubangiji yakan yi alheri da kuma daraja;

ba ya hana kowane abu mai kyau

wa waɗanda suke aikata abin da yake daidai.

12 Ya Ubangiji Maɗaukaki,

mai albarka ne mutumin da ya dogara gare ka.

Veja também