Convicção
A convicção cristã é firmeza de fé que não se abala diante da oposição. É a certeza interior que compele a proclamar a verdade com ousadia, independentemente das consequências.
Ousadia para falar
Recebereis poder e sereis minhas testemunhas. A convicção do Espírito nos equipa para proclamar com coragem e sem vergonha.
Amma ku za ku karɓi iko sa’ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauka a kanku; za ku kuma zama shaiduna cikin Urushalima, da kuma cikin dukan Yahudiya da Samariya, zuwa kuma iyakar duniya."
Da suka ga ƙarfin halin Bitrus da Yohanna suka kuma gane cewa su marasa ilimi ne, talakawa kuma, sai suka yi mamaki suka kuma lura cewa waɗannan mutane sun kasance tare da Yesu.
Bitrus da sauran manzannin suka amsa suka ce, "Dole ne mu yi wa Allah biyayya a maimakon mutane!
Ku kuma yi addu’a domina, don duk sa’ad da na buɗe bakina, in sami kalmomi babu tsoro, don in sanar da asirin bishara, wadda nake jakadanta cikin sarƙoƙi. Ku yi addu’a don in iya yin shelarta babu tsoro, yadda ya kamata in yi.
Ba na jin kunyar bishara, gama ita ikon Allah ne domin ceton kowa da ya gaskata, da farko ga Yahudawa, sa’an nan ga Al’ummai.
Duk wanda ya ji kunyata, da na kalmomina a wannan zamani na fasikanci da zunubi, Ɗan Mutum ma zai ji kunyarsa lokacin da ya shiga cikin ɗaukakar Ubansa, tare da tsarkakan mala’iku."
Saboda haka kada ka ji kunyar ba da shaida game da Ubangijinmu, ko kuwa ka ji kunyata, ni da nake ɗan sarƙa saboda shi. Sai dai ka haɗa kai tare da ni cikin shan wahala saboda bishara ta wurin ikon Allah,
Waɗannan kam, su ne abubuwan da ya kamata ka koyar, ka ƙarfafa ka kuma tsawata da dukan iko. Kada ka yarda wani yă rena ka.
Firmeza e confiança
Não temas diante dos homens. A Palavra de Deus é fogo na boca do profeta e firmeza na vida do crente.
Amma Ubangiji ya ce mini, "Kada ka ce, ‘Ni ɗan yaro ne kawai.’ Dole ka je wurin kowane mutumin da na aike ka ka kuma faɗa abin da na umarce ka.
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Sihiyona,
ka haura a bisa dutse.
Kai da ka kawo labari mai daɗi wa Urushalima,
ka tā da muryarka ka yi ihu,
ka ɗaga ta, kada ka ji tsoro;
faɗa wa garuruwan Yahuda,
"Ga Allahnku!"
Ubangiji Mai Iko Duka ya ba ni harshen umarni,
don in san maganar da za tă ƙarfafa gajiyayye.
Ya farkar da ni da safe,
ya farkar da kunnena don in saurara kamar wanda ake koya masa.
Zan sa goshinka ya zama da tauri kamar dutse, da tauri fiye da dutsen ƙanƙara ƙarfi. Kada ka ji tsoronsu ko ka firgita ta wurinsu, ko da yake su gidan ’yan tawaye ne."
Zan yi maganar farillanka a gaban sarakuna
ba kuwa za a kunyata ni ba,
Ku yi irin rayuwa mai kyau a cikin masu bautar gumaka, yadda ko da sun zarge ku da yin laifi, za su iya ganin ayyukanku nagari, su ɗaukaka Allah a ranar da zai ziyarce mu.
Jin tsoron mutum tarko ne,
amma duk wanda ya dogara ga Ubangiji zai zauna lafiya.
A maimako haka, muna magana ne kamar mutanen da Allah ya amince yă danƙa musu amanar wannan bishara. Ba ma ƙoƙari mu gamshi mutane sai dai Allah, mai auna zukatanmu.
"Ku ne hasken duniya. Birnin da yake a bisan tudu ba ya ɓoyuwa. Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.