Crianças
As crianças ocupam lugar especial no coração de Deus. A Bíblia instrui a educá-las, protegê-las e ensiná-las nos caminhos do Senhor desde cedo — formando gerações que temem a Deus.
Herança do Senhor
Os filhos são herança do Senhor. Eles são presentes de Deus — cada criança é um milagre e uma responsabilidade sagrada.
’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,
yara lada ne daga gare shi.
Ta haka ’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu
za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su,
’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai
da sassaƙa don adon fada.
Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?
Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.
Yaya matashi zai kiyaye hanyarsa da tsabta?
Sai ta yin rayuwa bisa ga maganarka.
Ku zo, ’ya’yana, ku saurare ni;
zan koya muku tsoron Ubangiji.
Instruir as crianças
Instrui a criança no caminho em que deve andar. A educação cristã é mandamento repetido através de toda a Escritura.
Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
Ka hori yaro a hanyar da ya kamata yă bi,
kuma sa’ad da ya tsufa ba zai bar ta ba.
Wauta tana da yawa a zuciyar yara,
amma sandar horo zai kore ta nesa da su.
Wauta tana da yawa a zuciyar yara,
amma sandar horo zai kore ta nesa da su.
Duk wanda ba ya horon ɗansa ba ƙaunarsa yake yi ba,
amma duk mai ƙaunarsa yakan kula ya hore shi.
Ɗa mai hikima yakan mai da hankali ga umarnin mahaifinsa,
amma mai ba’a ba ya sauraran kwaɓi.
Ɗana, kada ka manta da koyarwata,
amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
gama za su ƙara maka tsawon rai da shekaru masu yawa
su kuma kawo maka wadata.
Ɗana, kada ka manta da koyarwata,
amma ka kiyaye umarnaina a cikin zuciyarka,
domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,
kamar yadda mahaifi yake yin wa ɗa da yake fariya da shi.
ya koya mini ya ce,
"Ka riƙe kalmomina da dukan zuciyarka;
ka kiyaye umarnaina za ka kuwa rayu.
Ka nemi hikima, ka nemi fahimi;
kada ka manta da kalmomina ko ka kauce daga gare su.
Disciplinar com amor
A vara e a repreensão dão sabedoria. A disciplina produz o fruto pacífico da justiça nos que são exercitados por ela.
Sandar gyara kan ba da hikima,
amma yaron da aka bari ba horo kan jawo kunya ga mahaifiyarsa.
Kada ka bar yaro ba horo;
in ka yi masa horo da sanda, ba zai mutu ba.
Ka kasa kunne ga mahaifinka, wanda ya ba ka rai,
kada kuwa ka rena mahaifiyarka sa’ad da ta tsufa.
Ka saye gaskiya kada kuwa ka sayar da ita;
ka nemi hikima, horo da fahimi.
Duk wanda ya yi wa mahaifinsa fashi ya kuma kori mahaifiyarsa
ɗa ne da kan kawo kunya da wulaƙanci.
Gara matalauci wanda yake marar laifi
da wawa wanda leɓunansa masu ƙarya ne.
Mai adalci kan yi rayuwa marar abin zargi;
masu albarka ne ’ya’yan da za su biyo bayansa.
Akan san ƙananan yara ta ayyukansu,
ana iya sani ko rayuwarsu amintattu ne, mai nagarta.
Da yake wawa yakan kawo baƙin ciki ga mahaifinsa
da ɓacin rai ga wanda ya haife shi.
Jikoki rawanin tsofaffi ne,
kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
Jikoki rawanin tsofaffi ne,
kuma iyaye su ne abin taƙamar ’ya’yansu.
Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa,
amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.
Ɗa mai hikima kan kawo farin ciki wa mahaifinsa,
amma wawa yakan rena mahaifiyarsa.
Duk wanda ya kiyaye doka ɗa ne mai la’akari,
amma wanda yake abokantaka da masu zari yakan jawo wa mahaifinsa kunya.
Ɗana, ka saurari umarnin mahaifinka
kada kuma ka ƙyale koyarwar mahaifiyarka.
Za su zama kayan ado don su inganta ka
da kuma sarƙar wuya don su yi wa wuyanka ado.
"Yanzu fa, ’ya’yana, ku saurare ni;
masu albarka ne waɗanda suke kiyaye hanyoyina.
Ku saurari umarnina ku kuma zama masu hikima;
kada ku ƙyale ta.
Obediência e promessa
Filhos, obedecei a vossos pais no Senhor. Honra a teu pai e tua mãe para que viva muito tempo sobre a terra.
Ku ’ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku, gama ku na Ubangiji, abin da ya dace ku yi ke nan. Doka ta farko wadda aka haɗa da alkawari ita ce, "Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, don ka zauna lafiya, ka kuma yi tsawon rai a duniya."
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
Ku kuma iyaye, kada ku tsokane ’ya’yanku. Ku yi musu reno mai kyau. Ku koyar da su, ku kuma gargaɗe su game da Ubangiji.
Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ’ya’ya,
’Ya’ya, ku yi biyayya ga iyayenku cikin kome, gama wannan yakan gamshi Ubangiji.
Ubanni, kada ku matsa wa yaranku lamba, don kada su fid da zuciya.
Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku. Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
Ku koya wa ’ya’yanku su da himma. Yi musu magana game da su sa’ad da kuke zaune a gida, da sa’ad da kuke tafiya a hanya, sa’ad da kuke kwance, da sa’ad da kuka tashi.
Ku kiyaye ƙa’idodi da umarnai, waɗanda nake ba ku a yau, domin zaman lafiyarku da kuma na zuriyarku bayan ba ku, domin kuma ku yi tsawon rai a ƙasa wadda Ubangiji Allahnku yake ba ku har abada.
Ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan waɗannan umarnan da nake ba ku, da kuma ’ya’yanku, don ku zauna lafiya, da ku da ’ya’yanku a bayanku, gama za ku riƙa aikata abin da yake daidai da kuma yake mai kyau a gaban Ubangiji Allahnku.
ya ce musu, "Ku riƙe dukan kalmomin da na furta muku a yau, don ku umarce ’ya’yanku su lura, su yi biyayya da dukan kalmomin wannan doka. Ba kalmomi kurum ba ne dominku, amma har ranku ma. Ta wurinsu za ku yi tsawon rai a ƙasar da kuke haye Urdun ku ci gādonta."
Crianças e o reino
Deixai vir a mim as crianças. Jesus honrou as crianças como modelo de fé e humildade para todo o seu povo.
Yesu ya ce, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne."
Yesu ya ce, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin sama na irin waɗannan ne."
A lokacin nan sai almajirai suka zo wurin Yesu suka yi tambaya suka ce, "Wane ne mafi girma a mulkin sama?"
Sai ya kira ƙaramin yaro ya sa shi yă tsaya a tsakiyarsu. Sai ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama.
Sai ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in ba kun canja kuka zama kamar ƙananan yara ba, labudda, ba za ku shiga mulkin sama ba. Saboda haka, duk wanda ya ƙasƙantar da kansa kamar wannan yaro, shi ne mafi girma a mulkin sama. Duk kuma wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan a cikin sunana ya karɓe ni ne.
"Ku lura, kada ku rena ɗaya daga cikin waɗannan ƙanana. Gama ina faɗa muku mala’ikunsu a sama kullum suna duban fuskar Ubana da yake cikin sama.
A wannan lokaci sai Yesu ya ce, "Ina yabonka, Uba, Ubangijin sama da ƙasa, gama ka ɓoye waɗannan abubuwa ga masu hikima da masu ilimi, ka kuma bayyana su ga ƙananan yara.
Masu albarka ne waɗanda suke masu ƙulla zumunci,
gama za a kira su ’ya’yan Allah.
Mutane suka kawo ƙananan yara wurin Yesu don yă taɓa su, amma almajiran suka kwaɓe su. Da Yesu ya ga haka, sai ya yi fushi, ya ce musu, "Ku bar yara ƙanana su zo wurina, kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne.
Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu, "Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa."
Yesu kuwa ya yi girma, ya kuma ƙaru cikin hikima, ya kuma sami tagomashi a wurin Allah da mutane.
Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, "Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?"
Ya ce, "I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka."
Yesu ya ce, "Ciyar da ’ya’yan tumakina."
Identidade e crescimento
Somos filhos de Deus pelo Espírito de adoção. Crescer em Cristo é amadurecer em fé, obediência e amor ao próximo.
Duk da haka dukan waɗanda suka karɓe shi, ga waɗanda suka gaskata a sunansa, ya ba su iko su zama ’ya’yan Allah
Domin waɗanda Ruhun Allah yake bi da su ne ’ya’yan Allah.
Gama ba ku karɓi ruhun da ya mai da ku bayi da za ku sāke jin tsoro ba ne, sai dai kun karɓi Ruhun zaman ɗa. Ta wurinsa kuwa muke kira, "Abba, Uba."
Ruhu kansa yana ba da shaida tare da ruhunmu cewa mu ’ya’yan Allah ne.
Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah.
Dukanku ’ya’yan Allah ne ta wurin bangaskiya cikin Kiristi Yesu. Gama dukanku da aka yi muku baftisma cikin Kiristi, kuna sanye da Kiristi ke nan.
Dubi irin ƙaunar da Uba ya ƙaunace mu da ita mana, har ana ce da mu ’ya’yan Allah! Haka kuwa muke! Dalilin da ya sa duniya ba tă san mu ba shi ne, don ba tă san shi ba.
Abokaina ƙaunatattu, yanzu, mu ’ya’yan Allah ne, kuma abin da za mu zama nan gaba ba a riga an bayyana ba. Sai dai mun san cewa sa’ad da Kiristi ya bayyana, za mu zama kamar sa, domin za mu gan shi kamar yadda yake. Duk mai wannan bege a cikinsa yakan tsarkake kansa, kamar yadda shi Kiristi yake da tsabta.
Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu,
domin an gafarta muku zunubanku saboda sunansa.
’Ya’yana ƙaunatattu, ku yi nesa da gumaka.
Dole yă iya tafiyar da iyalinsa da kyau, yă kuma tabbata cewa ’ya’yansa suna yin masa biyayya da ladabin da ya dace.
In wani bai kula da danginsa ba, musamman iyalinsa na kurkusa, ya mūsunta bangaskiya ke nan, ya kuma fi marar ba da gaskiya muni.
Kun kuma manta da kalmar ƙarfafawan nan da tana ce da ku ’ya’ya,
"Ɗana kada ka rena horon Ubangiji,
kada kuma ka fid da zuciya sa’ad da ya kwaɓe ka,
domin Ubangiji yakan hori waɗanda yake ƙauna,
yakan kuma hori duk wanda yakan karɓa a matsayin ɗa."
Ku jimre shan wahala a matsayin horo; Allah yana yi da ku kamar ’ya’ya. Gama wane ɗa ne mahaifinsa ba ya horonsa? In ba a hore ku ba (kowa kuwa yakan sami horo), to, ku shegu ne ba ’ya’yan gida ba. Ban da haka ma, dukanmu mun kasance da ubannin jiki waɗanda suka hore mu muka kuma yi musu ladabi. Ashe, bai kamata mu yi wa Uban ruhohinmu biyayya mu kuwa rayu ba!
Babu horon da yake da daɗi a lokacin da ake yinsa, sai dai zafi. Amma daga baya waɗanda suka horu ta haka sukan sami kwanciyar rai wadda aikin adalci yake bayarwa.
Suka amsa suka ce, "Ka gaskata da Ubangiji Yesu, za ka sami ceto, kai da iyalinka."
Ka yi nesa da mugayen sha’awace-sha’awace na ƙuruciya, ka kuma bi adalci, bangaskiya, ƙauna da kuma salama, tare da waɗanda suke kira ga Ubangiji daga zuciya mai tsabta.
Abubuwan da ka ji na faɗa a gaban shaidu masu yawa kuwa ka danƙa wa amintattun mutane waɗanda su ma za su iya koya wa waɗansu.
Transmitir a fé
Contaremos à geração vindoura os louvores do Senhor. O legado de fé é o maior presente que damos aos nossos filhos.
Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza,
da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.
Ubangiji zai koya wa dukan ’ya’yanki maza,
da girma kuma salamar ’ya’yanki zai zama.
Masu rai, masu rai, su suke yabonka,
kamar yadda nake yi a yau;
iyaye za su faɗa wa ’ya’yansu
game da amincinka.
"Yana yiwuwa mahaifiya ta manta da jariri a ƙirjinta
ta kuma kāsa nuna tausayi ga yaron da ta haifa?
Mai yiwuwa ta manta,
amma ba zan taɓa manta da ke ba!
Duba, na zāna ki a tafin hannuwana;
katangarki kullum suna a gabana.
Bayan na dudduba abubuwa, sai na miƙe tsaye na ce wa manyan gari da shugabanni da kuma sauran jama’a, "Kada ku ji tsoronsu. Ku tuna da Ubangiji, wanda yake mai girma da banrazana, ku yi yaƙi don ’yan’uwanku, da ’ya’yanku maza da mata, da matanku da kuma gidajenku."
Yaron nan Sama’ila ya yi hidima a gaban Ubangiji a ƙarƙashin Eli. A waɗannan kwanaki kuwa jin magana daga wurin Ubangiji ba safai ba, babu kuma wahayi da yawa.
Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.
Ba abin da ya fi sa ni farin ciki fiye da in ji cewa ’ya’yana suna cikin gaskiyan nan.
Ba za mu ɓoye su wa ’ya’yanmu ba;
za mu faɗa wa tsara mai zuwa
ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,
ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.
Ya kafa ƙa’idodi wa Yaƙub
ya kuma kafa doka a cikin Isra’ila,
wadda ya umarce kakanni-kakanninmu
su koya wa ’ya’yansu,
don tsara na biye su san su,
har da ’ya’yan da ba a riga an haifa ba,
su kuma su faɗa wa ’ya’yansu.
Ta haka za su dogara ga Allah
ba kuwa za su manta da ayyukansa ba
amma za su kiyaye umarnansa.