Egoísmo
O egoísmo é o oposto do amor cristão. Jesus nos ensinou a negar a nós mesmos, tomar a cruz e segui-lo. A vida cristã é vida de entrega, serviço e generosidade.
Negar-se a si mesmo
Se alguém quer vir após mim, negue-se a si mesmo. O caminho de Cristo é o caminho da auto-entrega e do serviço.
Sai ya kira taron wurinsa tare da almajiransa ya ce, "Duk wanda zai bi ni, dole yă ƙi kansa, yă ɗauki gicciyensa yă bi ni.
Na biyun ita ce, ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’ Ba wata doka da ta fi waɗannan."
An gicciye ni tare da Kiristi. Yanzu ba ni ne nake raye ba, Kiristi ne yake raye a cikina. Rayuwar da nake yi a jiki, ina rayuwa ce ta wurin bangaskiya cikin Ɗan Allah, wanda ya ƙaunace ni ya kuma ba da kansa domina.
Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.
Amma ni ban ɗauki raina a bakin kome ba, in dai zan iya gama tserena in kuma kammala aikin da Ubangiji Yesu ya ba ni aikin shaida bisharar alherin Allah.
Viver para os outros
Ninguém busque o próprio interesse, mas o do próximo. O amor não busca os seus próprios interesses.
Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma.
Ƙauna tana da haƙuri, ƙauna tana da kirki. Ba ta kishi, ba ta burga, ba ta da girman kai. Ba ta rashin ladabi, ba ta sonkai, ba ta da saurin fushi, ba ta riƙe mutum a zuciya.
Kada ku ruɗi kanku. In waninku yana tsammani cewa yana da hikima, yadda duniya ta ɗauki hikima, to, sai ya mai da kansa "wawa" don yă zama mai hikima.
Ya kamata kowannenmu yă faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma yă gina shi.
Mutum mai kyauta zai azurta;
shi da yakan taimake waɗansu, za a taimake shi.
Wawa ba ya sha’awa ya sami fahimta
amma abin da yake so ya yi kaɗai, shi ne ya ba da ra’ayinsa.
Ka juye zuciyata wajen farillanka
ba wajen riba ta sonkai ba.
Gama inda akwai kishi da sonkai, a can za a tarar da hargitsi da kowane irin mugun aiki.