Sinais do fim dos tempos
A Bíblia descreve sinais que precederão a volta de Jesus. Guerras, falsos mestres, sinais cósmicos e a pregação do evangelho a todas as nações — tudo aponta para o fim dos tempos.
Sinais proféticos
Este evangelho do Reino será pregado em todo o mundo e então virá o fim. Os sinais dos últimos tempos já se manifestam.
Za a kuma yi wa’azin wannan bisharar mulki a cikin dukan duniya, yă zama shaida ga dukan al’ummai, sa’an nan ƙarshen yă zo.
"Nan da nan bayan tsabar wahalan nan
" ‘sai a duhunta rana,
wata kuma ba zai ba da haskensa ba;
taurari kuma za su fāffāɗi daga sararin sama,
za a kuma girgiza abubuwan sararin sama.’
"A sa’an nan ne alamar dawowar Ɗan Mutum zai bayyana a sararin sama, dukan al’umman duniya kuwa za su yi kuka. Za su ga Ɗan Mutum yana zuwa kan gizagizan sararin sama, da iko da kuma ɗaukaka mai girma. Zai kuwa aiki mala’ikunsa su busa ƙaho mai ƙara sosai, za su kuwa tattaro zaɓaɓɓunsa daga kusurwoyi huɗun nan, daga wannan bangon duniya zuwa wancan.
"Saboda haka sai ku zauna a faɗake, gama ba ku san a wace rana ce Ubangijinku zai zo ba. Ku dai gane wannan, da maigida ya san ko a wane lokaci ne da dare, ɓarawo zai zo, da sai yă zauna a faɗake yă kuma hana a shiga masa gida. Saboda haka ku ma, sai ku zauna a faɗake, domin Ɗan Mutum zai zo a sa’ar da ba ku za tă ba.
kuna kuma koya musu, su yi biyayya da duk abin da na umarce ku, kuma tabbatacce, ina tare da ku kullum, har ƙarshen zamani."
"Game da wannan rana ko sa’a kuwa, ba wanda ya sani, ko mala’ikun da suke sama, ko Ɗan, sai Uban kaɗai.
Os últimos dias
Nos últimos dias virão tempos difíceis, homens amantes de si mesmos. Mas derramarei o meu Espírito sobre toda a carne.
Amma fa ka san wannan, za a yi lokutan shan wahala a kwanakin ƙarshe. Mutane za su zama masu son kansu, masu son kuɗi, masu taƙama, masu girman kai, masu zage-zage, marasa biyayya ga iyayensu, marasa godiya, marasa tsarki, marasa ƙauna, marasa gafartawa, masu ɓata sunayen waɗansu, marasa kamunkai, masu ƙeta, marasa ƙaunar nagarta, masu cin amana, marasa hankali, waɗanda sun cika da ɗaga kai, masu son jin daɗi a maimakon ƙaunar Allah suna riƙe da siffofin ibada, amma suna mūsun ikonta. Kada wani abu yă haɗa ka da su.
"Allah ya ce, ‘A kwanakin ƙarshe,
zan zubo Ruhuna bisa dukan mutane.
’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,
samarinku za su ga wahayoyi,
dattawanku kuma za su yi mafarkai.
Kai, har ma a kan bayina, maza da mata,
zan zubo Ruhuna a waɗancan kwanaki,
za su kuwa yi annabci.
Zan nuna abubuwan banmamaki a sararin sama
da alamu a nan ƙasa,
jini da wuta da kuma hauhawan hayaƙi.
Za a mai da rana duhu,
wata kuma ya zama jini,
kafin zuwa rana mai girma da kuma ta ɗaukaka ta Ubangiji.
Kuma duk wanda ya kira
bisa sunan Ubangiji zai sami ceto.’
"Daga baya kuma,
zan zuba Ruhuna a bisan dukan mutane.
’Ya’yanku maza da mata za su yi annabci,
tsofaffinku za su yi mafarkai,
matasanku za su ga wahayoyi.
Har ma a bisan bayina, maza da mata,
zan zuba Ruhuna a kwanakin nan.
"A wannan lokaci Mika’ilu, babban mai mulki wanda yake kāre mutanenka, zai tashi. Za a yi lokacin matsananciyar wahala wanda ba a taɓa yi tun farkon ƙasashe har zuwa yanzu. Amma a lokacin da mutanenka, kowane mutum wanda aka sami sunansa a rubuce a cikin littafin, za a cece shi. Ɗumbun mutanen da suka yi barci cikin turɓayar duniya za su farka, waɗansu zuwa ga rai madawwami, waɗansu zuwa ga madawwamiyar kunya da kuma madawwamin ƙasƙanci. Waɗanda suke da hikima za su haskaka kamar hasken samaniya, waɗanda kuma suka jagoranci waɗansu da yawa zuwa adalci, za su zama kamar taurari har abada abadin.
Esperança e prontidão
O dia do Senhor virá como ladrão. Mas nós não somos das trevas — estejamos sóbrios, vigiliando e esperando.
Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban mala’ika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.
Saboda haka fa, kada mu zama kamar saura, waɗanda suke barci, sai dai mu zama masu tsaro da masu kamunkai. Gama masu barci, da dad dare suke barci, masu sha su bugu kuwa, da dad dare suke buguwa. Amma da yake mu na rana ne, bari mu zama masu kamunkai, sanye da bangaskiya da ƙauna kamar sulke, begen cetonmu kuma kamar hular kwano. Gama Allah bai naɗa mu don mu sha fushi ba, sai dai mu sami ceto ta wurin Ubangijinmu Yesu Kiristi.
"Ku lura fa don kada son jin daɗi na banza, da shaye-shaye, da damuwa na rayuwa su rinjayi zuciyarku, har ranar ta auko muku ba tsammani kamar tarko. Gama za tă zo a kan kowa da yake kan dukan duniya. Ku yi tsaro kullum, ku yi addu’a don ku iya kuɓuta daga dukan waɗannan abubuwa da suke kusan faruwa, don ku iya tsayawa a gaban Ɗan Mutum."
Amma kada ku manta da wannan abu guda ɗaya, abokaina ƙaunatattu. Ga Ubangiji kwana ɗaya kamar shekaru dubu ne, shekaru dubu kuma kamar kwana ɗaya ne. Ubangiji ba mai jinkiri ba ne wajen cika alkawarinsa, yadda waɗansunku suka fahimci jinkiri. Yana haƙuri da ku, ba ya so wani yă hallaka, sai dai kowa yă kai ga tuba.
Amma ranar Ubangiji za tă zo kamar ɓarawo. Sammai za su ɓace da ruri, abubuwan da suke cikinsu za su ƙone, ƙasa kuma da dukan abin da yake cikinta za su tonu.
Da yake za a hallaka dukan abubuwa ta haka, waɗanne irin mutane ne ya kamata ku zama? Ya kamata ku yi rayuwar tsarki da ta tsoron Allah, yayinda kuke zuba ido ga zuwan ranar Allah kuna gaggauta zuwanta. Wannan rana za tă kawo wa sammai hallaka ta ƙunan wuta, abubuwa kuma za su narke don zafi. Amma bisa ga alkawarinsa muna zuba ido ga sabuwar sama da kuma sabuwar ƙasa, inda adalci zai yi zama.
Ku saurara, in gaya muku wani asiri. Ba dukanmu ne za mu yi barci ba, sai dai duk za a sauya kamanninmu farat ɗaya, cikin ƙyaftawar ido, da busan ƙaho na ƙarshe. Gama za a busa ƙaho, za a tā da matattu da jiki irin da ba ya ruɓewa, za a kuma sauya kamanninmu.
"Ga shi, na halicci
sabuwar sama da kuma sabuwar duniya.
Abubuwa na dā za a manta da su,
ba kuwa za a ƙara tuna da su ba.
Amma ku yi murna ku kuma yi farin ciki har abada
a abin da na halitta,
gama zan halicci Urushalima ta zama abin murna
mutanenta kuwa abin farin ciki.
Zan yi farin ciki a kan Urushalima
in kuma yi murna saboda mutanena;
a can ba za a ƙara jin
karar makoki da na kuka ba.
"Tabbatacce rana tana zuwa; za tă yi ƙuna kamar wutar maƙera. Dukan masu girman kai da kowane mai aikata mugunta zai zama ciyawa, wannan rana mai zuwa za tă ƙone su. Babu saiwa ko reshen da za a bar musu," in ji Ubangiji Maɗaukaki. Amma ku da kuke girmama sunana, ranar adalci za tă fito tare da warkarwa a fikafikanta. Za ku kuwa fita kuna tsalle kamar ’yan maruƙan da aka sake daga garke.
Sa’an nan na ga sabon sama da sabuwar duniya, gama sama na farko da duniya ta farko sun shuɗe, babu kuma wani teku. Na ga Birni Mai Tsarki, sabuwar Urushalima tana saukowa daga sama, daga Allah, a shirye kamar amaryar da aka yi mata ado mai kyau saboda mijinta. Na kuma ji wata babbar murya daga kursiyin tana cewa, "Yanzu mazaunin Allah yana tare da mutane, zai kuma zauna tare da su. Za su zama mutanensa, Allah kansa kuwa zai kasance tare da su yă kuma zama Allahnsu. Zai share dukan hawaye daga idanunsu. Ba sauran mutuwa ko makoki ko kuka ko azaba, gama tsofaffin al’amura sun shuɗe."