Pular para o conteúdo
Publicidade

Milagres

Por Bíblia Online

Os milagres manifestam o poder soberano de Deus. Desde a criação até os sinais de Jesus e dos apóstolos, Deus intervém sobrenaturalmente na história para revelar sua glória e amor.

O Deus dos milagres

Para Deus nada é impossível. Ele abriu o mar, fez cair fogo do céu e ressuscitou mortos. Seu poder não tem limites.

Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne."

Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba ya yiwuwa, amma ga Allah kuwa, dukan abubuwa masu yiwuwa ne."

Gama ba abin da zai gagari Allah."

"Ni ne Ubangiji Allah na dukan yan adam. Akwai wani abin da ya gagare ni?

Da Musa ya miƙa hannunsa a bisa teku, sai Ubangiji ya tura teku baya da iskar gabas mai ƙarfi duk dare, ya maishe shi busasshiyar ƙasa. Ruwa ya rabu, sai Isra’ilawa suka wuce cikin teku a kan busasshiyar ƙasa, ruwan ya zama musu katanga dama da hagu.

Zan tuna da ayyukan Ubangiji;

I, zan tuna mu’ujizanka na tun .

Zan yi tunani a kan dukan ayyukanka

in lura da dukan manyan abubuwan da ka aikata.

Kai ne Allahn da yakan aikata mu’ujizai;

ka nuna ikonka a cikin mutane.

Milagres pela fé

Se tiverdes fé como um grão de mostarda, movereis montanhas. A fé é a chave que acessa o poder miraculoso de Deus.

Ya amsa ya ce, "Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, Matsa daga nan zuwa can,zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku."

Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiya, ba kuwa da wata shakka ba, ba kawai za ku iya yin abin da aka yi wa itacen ɓauren nan ba, amma za ku ma iya ce wa dutsen nan, Je ka, ka jefa kanka cikin teku,sai faru.

Yesu ya ce, " In za ka iya? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata."

Yesu ya kalle su ya ce, "Ga mutum kam, wannan ba mai yiwuwa ba ne, amma ga Allah, wannan mai yiwuwa ne; dukan abubuwa masu yiwuwa ne ga Allah."

Yesu ya amsa ya ce, "Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah."

Bai kuwa yi abubuwan banmamaki da yawa a can ba saboda rashin bangaskiyarsu.

Sinais e prodígios

Os apóstolos realizaram sinais e maravilhas em nome de Jesus. Os dons do Espírito incluem a operação de milagres e a fé sobrenatural.

"Mutanen Isra’ila, ku saurari wannan. Yesu Banazare shi ne mutumin da Allah ya tabbatar muku ta wurin mu’ujizai, ayyukan banmamaki, da kuma alamu, waɗanda Allah ya yi a cikinku ta wurinsa, kamar yadda ku kanku kuka sani.

Bayan suka yi addu’a, sai inda suka taru ya jijjigu. Dukansu kuwa suka cika da Ruhu Mai Tsarki, suka yi ta shaidar maganar Allah babu tsoro.

Allah ya yi ayyukan banmamakin da suka wuce misali ta hannu Bulus, har ma ana kai hankicif da adikan da suka taɓa jikinsa wa marasa lafiya, suka kuwa warke daga cututtukansu mugayen ruhohi kuma suka rabu da su.

Abubuwan da suke tabbatar da manzo, alamu, abubuwa da kuma ayyukan banmamaki, an aikata su a cikinku da matuƙar nacewa.

A cikin ikkilisiya, da farko dai Allah ya zaɓa waɗansu ya naɗa su su zama manzanni, na biyu annabawa, na uku malamai, sa’an nan masu yin ayyukan banmamaki, sai masu baiwar warkarwa, da masu taimakon waɗansu, da masu baiwar gudanarwa, sa’an nan kuma masu magana da harsuna iri-iri.

Ga wani, an ba shi saƙon hikima ta wurin Ruhu, ga wani baiwar saƙon sani ta wurin wannan Ruhu guda. Ga wani bangaskiya ta wurin wannan Ruhu, ga wani kuma baiwar warkarwa ta wurin wannan Ruhu guda. Ga wani yin ayyukan banmamaki, ga wani annabci, ga wani baiwar rarrabe ruhohi, ga wani baiwar magana da harsuna dabam-dabam, ga wani har wa yau iya fassarar harsuna.

Yesu ya ce, "Kada ku hana shi. Ba wanda yake yin ayyukan banmamaki a cikin sunana, nan take faɗi wani abu mummuna game da ni. Gama duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne.

Milagres de cura e provisão

A oração da fé salvará o enfermo. Deus provê, cura e intervém quando clamamos a Ele com fé genuína.

Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa. Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi. Ya sāke yin addu’a, sai sammai suka ba da ruwan sama, ƙasa kuma ta ba da amfaninta.

Sai Yesu ya ɗauki burodin biyar da kifin biyun, ya ɗaga kansa sama, ya yi godiya, ya kuma kakkarya su. Ya ba wa almajiransa, domin su rarraba wa mutanen. Duka kuwa suka ci suka ƙoshi. Almajiran suka kwashe ragowar gutsattsarin cike da kwanduna goma sha biyu.

Yesu ya warkar da mace gurguwa a ranar Asabbaci.

Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majami’a, a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan. Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, "Mace, an yantar da ke daga rashin lafiyarki." Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.

Amma mai mulkin majami’ar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, "Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba."

Ubangiji ya amsa masa ya ce, "Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba yakan kunce bijiminsa ko jakinsa, kai shi waje ba shi ruwa, a ranar Asabbaci ba? Ashe, bai kamata a yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?"

Sa’ad da ya faɗi wannan, sai duka masu gāba da shi suka kunyata. Amma mutane kuwa suka yi murna saboda dukan abubuwan banmamaki da yake yi.

Wannan shi ne na fari cikin abubuwan banmamakin da Yesu ya yi a Kana ta Galili. Ta haka ya bayyana ɗaukakarsa, almajiransa kuwa suka ba da gaskiya gare shi.

Bayan mutanen suka ga abin banmamakin da Yesu ya yi, sai suka fara cewa, "Lalle, wannan shi ne Annabin nan mai zuwa duniya."

Sai Yesu ya ce masa, "Wato ka gaskata saboda ka gan ni ne, masu albarka ne waɗanda ba su gan ni ba, amma suka gaskata."

Yesu ya yi waɗansu abubuwan banmamaki da yawa a gaban almajiransa da ba a rubuta a wannan littafi ba. An dai rubuta waɗannan ne don ku gaskata Yesu ne Kiristi, Ɗan Allah kuma ta wurin gaskatawa ku sami rai a cikin sunansa.

A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata. (Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu tashi daga matattu ba.)

Discernimento nos sinais

A Bíblia alerta contra falsos milagres e sinais enganosos. Devemos provar os espíritos e não seguir sinais que desviam de Deus.

Bautar waɗansu alloli

In wani annabi ko mai mafarkai, ya bayyana a cikinku, ya kuma yi muku shelar wata alama mai banmamaki ko al’ajabi, in kuwa alamar, ko al’ajabin da annabin ya yi faɗin ya faru, ya kuma ce, "Bari mu bi waɗansu alloli (allolin da ba ku sani ba) mu kuma yi musu sujada," kada ku saurari kalmomin wannan annabi ko mai mafarki. Ubangiji Allahnku yana gwada ku ne don sani ko kuna ƙaunarsa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku. Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.

Sa’an nan na ga mugayen ruhohi guda uku da suka yi kamar kwaɗi; suka fito daga bakin macijin nan, da kuma daga bakin dabbar, da kuma daga bakin annabin ƙaryan nan. Su ruhohin aljanu ne da suke aikata abubuwan banmamaki, sukan je wurin sarakunan dukan duniya, don su tattara su don yaƙi a babbar ranar Allah Maɗaukaki.

Alamar Yunana

Sa’an nan waɗansu Farisiyawa da malaman dokoki suka ce masa, "Malam, muna so mu ga wata alama mai banmamaki daga gare ka."

Sai ya amsa ya ce, "Mugaye da masu zinan zamanin nan suna neman wata alama mai banmamaki! Amma babu wadda za a nuna musu, sai dai alama ta annabi Yunana. Gama kamar yadda Yunana ya yi yini uku da kuma dare uku a cikin wani babban kifi, haka Ɗan Mutum zai yi yini uku da kuma dare uku a cikin ƙasa.

Kaiton biranen da ba su tuba ba

Sai Yesu ya fara yin tir da biranen da aka yi yawancin ayyukansa na banmamaki, don ba su tuba ba. "Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka. Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku. Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har zuwa yau. Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a."

A criação como milagre

O próprio corpo humano é milagre de Deus. Toda a criação testifica do poder e da sabedoria do Criador.

Gama ka halicci ciki-cikina;

ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.

Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;

ayyukanka suna da banmamaki,

na san da haka sosai.

Zan yabe ka, ya Ubangiji, da dukan zuciyata;

zan faɗa dukan abubuwan banmamakinka.

Saboda haka Ubangiji kansa zai ba ku alama. Ga shi budurwa za yi ciki, za haifi ɗa, za kuwa kira shi Immanuwel.

Duk wannan ya faru ne, don a cika abin da Ubangiji ya faɗi ta bakin annabin cewa, "Ga shi budurwa za yi ciki, za haifi ɗa, kuma za a kira shi Immanuwel" (wanda yake nufin "Allah tare da mu").

amma da suka gan shi yana takawa a kan tafkin, sai suka yi tsammani fatalwa ce. Sai suka yi ihu, domin dukansu sun gan shi, suka kuma tsorata.

Nan da nan ya yi magana da su ya ce, "Ku yi ƙarfin hali! Ni ne. Kada ku ji tsoro."

Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, "Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita."

Da ya yi kusa da wurin da hanyar ta gangara zuwa Dutsen Zaitun, sai dukan taron almajirai suka fara yabon Allah, da muryoyi masu ƙarfi, da murna, saboda dukan ayyukan banmamaki da suka gani. Suna cewa,

"Mai albarka ne sarki wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji!"

"Salama ta kasance a sama, da ɗaukaka kuma a can cikin sama!"

Bayan ya faɗi wannan, sai aka ɗauke shi sama a idanunsu sai wani girgije ya rufe shi daga ganinsu.

Sai na fāɗi a ƙasa na kuma ji wata murya ta ce mini, Shawulu! Shawulu! Don me kake tsananta mini?

Annobar fāra

Sai Ubangiji ya ce wa Musa, "Je wurin Fir’auna, gama na riga na taurare zuciyarsa da kuma zukatan fadawansa domin in aikata waɗannan mu’ujizai nawa a tsakiyarsu, don kuma ku gaya wa ya’yanku da jikokinku yadda na tsananta wa Masarawa, da kuma yadda na aikata mu’ujizai a cikinsu, don ku sani ni ne Ubangiji."

Seja o primeiro