Publicidade

Pecado

Por Bíblia Online

O pecado é a realidade que separa a humanidade de Deus. Mas a Bíblia também revela a solução: o sangue de Cristo que nos purifica e a graça que nos liberta de toda condenação.

A universalidade do pecado

Todos pecaram e carecem da glória de Deus. Não há justo, nem sequer um. O pecado entrou no mundo por um homem, mas a graça veio por Jesus.

gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah,

gama duka sun yi zunubi suka kuma kāsa ga ɗaukakar Allah, an kuma kuɓutar da su kyauta ta wurin alherinsa bisa ga aikin fansar da ya zo ta wurin Yesu Kiristi.

Saboda haka babu wanda Allah zai ce da shi mai adalci ta wurin kiyaye doka kawai; a maimako, ta wurin doka ne muke sane da zunubi.

Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma kyautar Allah rai madawwami ne a cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

Dukanmu mun zama kamar wanda yake marar tsabta,

kuma dukan ayyukanmu masu adalci sun zama kamar ƙazaman tsummoki;

duk mun zama kamar busasshen ganye,

kamar iska haka zunubanmu sukan share mu.

Duk mai yin zunubi yana karya doka ne; tabbatacce, zunubi, karya doka ne.

Liberdade da condenação

Não há condenação para os que estão em Cristo Jesus. Ele nos libertou da lei do pecado e da morte para vivermos em novidade de vida.

Rai ta wurin Ruhu

Saboda haka, yanzu babu hukunci don waɗanda suke cikin Kiristi Yesu, gama ta wurin Kiristi Yesu dokar Ruhu mai ba da rai ta yantar da ni daga Dokar Musa.

Saboda haka kada ku bar zunubi mallaki jikin nan naku mai mutuwa sa ku zama masu biyayya ga mugayen sha’awace-shaawacensa. Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci. Gama zunubi ba zai zama maigidanku ba, domin ba kwa ƙarƙashin doka, sai dai ƙarƙashin alheri.

Bayi ga adalci

Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan! Ba ku sani ba cewa sa’ad da kuka miƙa kanku ga wani don ku yi masa biyayya a matsayin bayi, ko ku bayi ne ga zunubi, wanda yake kai ga mutuwa, ko kuwa ga biyayya, wadda take kai ga adalci, ashe, ba kun zama bayi ga wannan da kuke yi wa biyayya ba ke nan? Amma godiya ga Allah don ko da yake a ku bayi ne ga ikon zunubi, da dukan zuciyarku kun yi biyayya ga irin koyarwar da aka danƙa muku. An yanta ku daga zunubi, kun kuma zama bayi ga aikin adalci.

Bayi ga adalci

Me za mu ce ke nan? Za mu ci gaba yin zunubi domin ba ma ƙarƙashin doka sai dai ƙarƙashin alheri? Sam, ko kaɗan!

Mun san cewa doka aba ce ta ruhu; amma ni ba na ruhu ba ne, an sayar da ni a matsayin bawa ga zunubi. Ban gane abin da nake yi ba. Don abin da nakan so yi, ba shi nakan yi ba, sai dai abin da nake ƙi, shi nake yi. In kuma na yi abin da ba na son yi, na yarda da cewa dokar aba ce mai kyau. Kamar dai yadda yake, ba ni kaina nake yinsa ba, sai dai zunubin da yake zaune a cikina ne.

Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, duk mai yin zunubi bawan zunubi ne.

Confissão e perdão

Se confessarmos os nossos pecados, Deus é fiel e justo para nos perdoar e purificar de toda injustiça. A confissão liberta a alma.

In muka ce ba mu da zunubi, muna ruɗin kanmu ne, gaskiya kuwa ba ta cikinmu. In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.

In muka furta zunubanmu, shi mai aminci ne, mai adalci kuma, zai gafarta mana zunubanmu, kuma tsarkake mu daga dukan rashin adalci.

In muka ce muna zumunci da shi amma muna tafiya cikin duhu, ƙarya muke yi, kuma ba ma rayuwa bisa ga gaskiya.

Ka yi mini jinƙai, ya Allah,

bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa;

bisa ga tausayinka mai girma

ka shafe laifofina.

Ka wanke dukan kurakuraina

ka tsarkake ni daga zunubina.

Kai kaɗai na yi wa zunubi

na yi abin da yake mugu a idonka,

ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana

aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.

Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa

mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.

Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki;

ka koya mini hikima a wuri can ciki.

Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab;

ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.

Bari in ji farin ciki da murna;

bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.

Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina

ka kuma shafe dukan kurakuraina.

Sa’an nan na furta zunubina a gare ka

ban kuwa ɓoye laifina ba.

Na ce, "Zan furta

laifofina ga Ubangiji."

Ka kuwa gafarta

laifin zunubina. Sela

Mai farin ciki ne shi

wanda aka gafarta masa laifofinsa,

wanda aka shafe zunubansa.

Saboda sunanka, ya Ubangiji,

ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne.

Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma,

gama suna nan tun .

Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata

da kuma hanyoyin tawayena;

bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni,

gama kai nagari ne, ya Ubangiji.

Wane ne zai iya rabe kurakuransa?

Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.

Duk wanda ya ɓoye zunubansa ba ya taɓa cin nasara,

amma duk wanda ya furta ya kuma ƙi su yakan sami jinƙai.

Vencendo o pecado

Cristo nos resgatou e nos restaurou. Devemos mortificar as obras da carne, fugir do pecado e prosseguir em santidade.

Shi kansa ya ɗauki zunubanmu a jikinsa a kan itace, domin mu mutu ga zunubai mu kuma rayu ga adalci; ta wurin raunukansa ne kuka sami warkarwa.

Za haifi ɗa, za ka kuma sa masa suna Yesu, yana ceto. gama shi ne zai ceci mutanensa daga zunubansu."

Shi da bai san zunubi ba, Allah ya mai da shi kamar hadayar zunubi saboda mu, domin mu sami adalcin Allah ta wurinsa.

haka aka miƙa Kiristi hadaya sau ɗaya domin ɗauke zunuban mutane masu yawa; zai kuma bayyana sau na biyu, ba don ɗauki zunubi ba, sai dai don kawo ceto ga waɗanda suke jiransa.

Duk mai aikata abin da yake zunubi shi na Iblis ne, domin Iblis mai aikata zunubi ne tun farko. Dalilin da ya sa Ɗan Allah ya bayyana kuwa shi ne don rushe aikin Iblis.

Mun san cewa kowane haifaffe na Allah ba ya cin gaba da yin zunubi; kasancewarsa haifaffe na Allah ita takan kāre shi, mugun kuwa ba zai iya cuce shi ba.

Saboda haka, sai ku fid da duk wani abin da yake kawo sha’awa a zukatanku, fasikanci, ƙazanta, sha’awa, muguwar sha’awa, da kuma kwaɗayi wanda shi ma bautar gumaka ne.

Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata, ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da mutane masu tsarki na Allah ba.

Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su. Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye.

"Cikin fushinku kada ku yi zunubi." Kada ku bar rana ta fāɗi kuna fushi,

Responsabilidade e restauração

O pecado tem consequências, mas Deus restaura o arrependido. Devemos corrigir uns aos outros com mansidão e cobrir o pecado com amor.

Yin alheri ga kowa

Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba.

Yin alheri ga kowa

Yan’uwa, in an kama wani yana cikin yin zunubi, ku da kuke masu ruhaniya ya kamata ku komo da shi a kan hanya a hankali. Amma ku lura da kanku, domin kada maimakon dawowa da ɗan’uwanku, ku ma ku fāɗi cikin jarraba. Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.

Ɗan’uwa da ya yi maka laifi

"In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.

Ɗan’uwa da ya yi maka laifi

"In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.

"Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.

"Don me kake duban ɗan tsinken da yake idon ɗan’uwanka, alhali kuwa ga gungume a naka ido?

Gama in kuna yafe wa mutane sa’ad da suka yi muku laifi, Ubanku da yake cikin sama ma zai gafarta muku.

Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

Saboda haka, duk wanda ya san abu mai kyan da ya kamata yi, bai kuwa yi ba, ya yi zunubi ke nan.

Ku matso kusa da Allah shi kuwa zai matso kusa da ku. Ku wanke hannuwanku, ku masu zunubi, ku kuma tsarkake zukatanku, ku masu zuciya biyu.

Ku mazinata, ba ku san cewa abokantaka da duniya gāba ce da Allah ba? Duk wanda ya zaɓa zama abokin duniya ya zama abokin gāban Allah ke nan.

Daga wannan baki guda yabo da la’ana suke fitowa. Yan’uwana, wannan bai kamata zama haka ba.

Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

Fuga do pecado

Bem-aventurado o que não anda no conselho dos ímpios. O caminho do justo é guardado pelo Senhor, e sua Palavra nos protege da queda.

Mai farin ciki ne mutumin

da ba ya aiki da shawarar mugaye

ko yi abin da masu zunubi suke yi

ko zauna tare da masu yin ba’a.

Ka bi da sawuna bisa ga maganarka;

kada ka bar zunubi mallake ni.

Mai mutunci yana tafiya lafiya,

amma shi da yake tafiya a karkatattun hanyoyi za a kama shi.

Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne."

Ba ku sani ba cewa mugaye ba za su gāji mulkin Allah ba? Kada fa a ruɗe ku. Ba masu fasikanci ko masu bautar gumaka ko masu zina ko karuwan maza, ko yan daudu, ko ɓarayi ko masu kwaɗayi ko mashaya ko masu ɓata suna ko masu zamba da za su gāji mulkin Allah.

Bilatus kuwa ya sāke fitowa ya ce wa Yahudawa, "Ga shi, zan fito muku da shi don ku san cewa ban same shi da wani abin zargi ba." Sa’ad da Yesu ya fito sanye da rawanin ƙayar da kuma riga mai ruwan shunayya, sai Bilatus ya ce musu, "Ga mutumin!"

Nan da nan da manyan firistoci da ma’aikatansu suka gan shi, sai suka yi ihu suka ce, "A gicciye! A gicciye!"

Amma Bilatus ya amsa ya ce, "Ku, ku ɗauke shi ku gicciye. Ni dai ban same shi da wani abin zargi ba."

Duk wanda kuka gafarta wa zunubansa, an gafarta masa ke nan. Duk wanda ba ku gafarta wa ba kuwa, ba a gafarta masa ba ke nan."

Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi."

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-