Pular para o conteúdo
Publicidade

Seguir a Jesus

Por Bíblia Online

Seguir a Jesus é o convite mais transformador da Bíblia. Jesus chamou pescadores, cobradores de impostos e pessoas comuns para deixar tudo e segui-lo. Esse chamado continua vivo hoje.

O chamado de Jesus

Jesus disse: 'Segue-me'. Esse convite simples e poderoso mudou a vida de pescadores, publicanos e pessoas comuns ao longo da história.

Sai Yesu ya ce, "Zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masu jan mutane zuwa wurina." Nan da nan suka bar abin kamun kifinsu suka bi shi.

Kiran Mattiyu

Da Yesu ya yi gaba daga wurin, sai ya ga wani mutum mai suna Mattiyu zaune a inda ake karɓar haraji. Ya ce masa, "Bi ni." Mattiyu kuwa ya tashi ya bi shi.

Yesu ya kira Filibus da Natanayel

Kashegari Yesu ya yanke shawara tafi Galili. Da ya sami Filibus sai ya ce masa, "Bi ni."

Wahalar bin Yesu

Suna kan tafiya a hanya, sai wani mutum ya ce masa, "Zan bi ka, duk inda za ka."

Yesu ya ce, "Yanyawa suna da ramummuka, tsuntsayen sararin sama suna da sheƙuna, amma Ɗan Mutum ba shi da wurin da zai sa kansa."

Ya kuma ce wa wani mutum, "Ka bi ni."

Amma mutumin ya amsa ya ce, "Ubangiji, bari in je in binne mahaifina tukuna."

Yesu ya ce masa, "Ka bar matattu su binne matattunsu, amma kai, ka je ka yi shelar mulkin Allah."

Har wa yau, wani ya ce, "Zan bi ka, Ubangiji, amma ka bar ni in je in yi bankwana da iyalina tukuna."

Yesu ya amsa ya ce, "Babu wani da yakan sa hannunsa a garman shanu, sa’an nan ya waiwaya baya, da ya isa ya shiga hidima a cikin mulkin Allah ba."

O custo do discipulado

Seguir a Jesus exige renúncia. É preciso tomar a cruz diariamente, deixar tudo para trás e amar a Cristo acima de qualquer outro vínculo.

Sa’an nan Yesu ya ce wa almajiransa, "Duk mai son bina, dole ƙi kansa, ɗauki gicciyensa, bi ni.

"Duk wanda yakan zo wurina, amma bai ƙi mahaifinsa da mahaifiyarsa, da matarsa da ya’yansa, da yan’uwansa mata da maza, kai, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. Kuma duk wanda ba yakan ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba.

Bitrus ya ce, "Mun bar kome domin mu bi ka!"

Yesu ya amsa ya ce, "Gaskiya nake gaya muku, babu wanda zai bar gida, ko yan’uwa maza da mata, ko mahaifiya, ko mahaifi, ko ya’ya, ko gonaki saboda ni, da kuma bishara, sa’an nan kāsa samun ninkinsu ɗari a zamanin yanzu (na gidaje, da yan’uwa mata, da yan’uwa maza, da uwaye, da ya’ya, da gonaki amma tare da tsanani) a lahira kuma sami rai madawwami. Amma da yawa da suke na farko, za su zama na ƙarshe, na ƙarshe kuma, za su zama na farko."

Caminhar com Cristo

Quem segue a Jesus não anda em trevas, mas tem a luz da vida. Ele nos convida a crescer nele e a servir como Ele serviu.

Gaskiyar shaidar Yesu

Sa’ad da Yesu ya sāke magana da mutanen, sai ya ce, "Ni ne hasken duniya. Duk wanda ya bi ni ba zai yi tafiya cikin duhu ba, sai dai sami hasken rayuwa."

Duk wanda zai bauta mini dole bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.

Ga wannan ne aka kira ku, domin Kiristi ya sha wahala dominku, ya bar muku gurbin da ya kamata ku bi.

"Bai taɓa yin laifi ba sam,

ba a kuma sami ƙarya a bakinsa ba."

Sa’ad da suka zazzage shi, bai rama ba; sa’ad da ya sha wahala, bai yi barazana ba. A maimakon haka, ya miƙa kansa ga wanda yake shari’ar adalci.

Ya kamata kullum ƙauna sa mu faɗa gaskiya. Ta haka za mu yi girma a kowace hanya, mu kuma zama kamar Kiristi, wanda yake kan

Dole ku kiyaye dokokina kuma ku lura ku bi farillaina. Ni ne Ubangiji Allahnku.

Seja o primeiro