Publicidade

Servir

Por Bíblia Online

Servir é o coração do evangelho. Jesus não veio para ser servido, mas para servir. O cristão é chamado a seguir esse exemplo, colocando-se a serviço de Deus e do próximo.

O exemplo de Jesus

Cristo é o modelo supremo de serviço. Ele lavou os pés dos discípulos e deu a própria vida como resgate por muitos.

Gama ko Ɗan Mutum ma, bai zo domin a bauta masa ba, amma don yi bauta, kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa."

kamar yadda Ɗan Mutum bai zo don a bauta masa ba, sai dai don yi bauta, kuma ba da ransa fansa saboda mutane da yawa."

Ba haka zai kasance da ku ba. Maimakon haka, duk mai son zama babba a cikinku, dole zama bawanku, kuma duk mai son zama shugaba, dole zama bawanku,

Da yake ni da nake Ubangijinku da kuma Malaminku, na wanke ƙafafunku, haka ku ma ya kamata ku wanke ƙafafun juna.

Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, "In wani yana so zama na fari, dole zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa."

Servindo ao Senhor

Servir a Deus é um privilégio e uma ordenança. Devemos amá-lo de todo coração e servi-lo com alegria e fidelidade.

Amma in kuka ga ba za ku iya bauta wa Ubangiji ba, sai ku zaɓa yau wanda za ku bauta masa, ko allolin da kakanninku suka bauta musu a hayin Kogin Yuferites, ko kuma allolin Amoriyawa, waɗanda kuke zama a cikin ƙasarsu. Amma da ni da gidana, Ubangiji ne za mu bauta wa."

Amma ku yi hankali, ku kiyaye umarnai da kuma dokokin da Musa bawan Ubangiji ya ba ku. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya kan hanyarsa, ku yi biyayya da umarnansa, ku riƙe shi sosai, ku bauta masa da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku."

Ku ji tsoron Ubangiji

Yanzu fa, ya Isra’ila, mene ne Ubangiji Allahnku yake so a gare ku, in ba ku ji tsoron Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin hanyoyinsa, ku ƙaunace shi, ku bauta wa Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, ku kuma kiyaye umarnan Ubangiji da kuma ƙa’idodinsa da nake ba ku a yau don amfaninku ba?

Ubangiji Allahnku ne za ku bi, shi ne kuma za ku girmama. Ku kiyaye umarnansa, ku kuma yi masa biyayya; ku bauta masa, ku kuma manne masa.

Kada ku zama marasa himma, sai dai masu himma a ruhaniyarku, kuna bauta wa Ubangiji.

balle jinin Kiristi, wanda ta wurin Ruhu madawwami ya miƙa kansa marar aibi ga Allah, ai, zai tsabtacce lamirinmu daga ayyukan da suke kai ga mutuwa, don mu bauta wa Allah mai rai!

Servir ao próximo

A liberdade cristã nos chama a servir uns aos outros pelo amor. Cada dom recebido é para edificação do corpo de Cristo.

Ku yan’uwana, an kira ku ga zama yantattu. Amma kada ku yi amfani da yancinku don aikata ayyukan mutuntaka a maimakon haka, ku yi hidimar juna da ƙauna.

Ku yi rayuwa kamar mutanen da aka yantar, sai dai kada ku yi amfani da yancinku a matsayin hujjar aikata mugunta; ku yi rayuwa kamar bayin Allah.

Duk wanda zai bauta mini dole bi ni, inda kuma nake, a can bawana zai kasance. Ubana zai girmama wanda yake bauta mini.

"Ba mai iya bauta wa iyayengiji biyu. Ko dai ƙi ɗaya, ƙaunaci ɗaya, ko kuwa yi aminci ga ɗaya, sa’an nan rena ɗayan. Ba dama ku bauta wa Allah, ku kuma bauta wa kuɗi gaba ɗaya."

Kada ku miƙa gaɓoɓin jikinku ga zunubi a matsayin kayan aikin mugunta, sai dai ku miƙa kanku ga Allah, a matsayin waɗanda aka fitar da su daga mutuwa zuwa rai; ku kuma miƙa gaɓoɓin jikinku gare shi a matsayin kayan aikin adalci.

Fidelidade e recompensa

O servo fiel e sábio será recompensado pelo Senhor. A fidelidade no serviço honra a Deus e produz frutos eternos.

"Maigidansa ya amsa ya ce, Madalla, bawan kirki mai aminci! Ka yi aminci a kan abubuwa kaɗan, zan sa ka lura da abubuwa masu yawa. Zo ka yi farin ciki tare da maigidanka!

Saboda haka, ƙaunatattu yan’uwana, ku tsaya da daram. Kada wani abu jijjiga ku. Ku ba da kanku kullum ga aikin Ubangiji, domin kun san cewa famar da kuke yi saboda Ubangiji ba a banza take ba.

Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci, domin mutumin Allah zama shiryayye sosai saboda kowane kyakkyawan aiki.

In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi,

zai sa sawu su kahu;

Ubangiji yakan cece bayinsa;

ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.

Seja o primeiro
Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-