Pular para o conteúdo
Publicidade

Vizinho

Por Bíblia Online

Amar o próximo é um dos mandamentos centrais do evangelho. A Bíblia nos ensina que nossos vizinhos são aqueles a quem devemos servir, apoiar e encorajar com amor genuíno.

O mandamento do amor ao próximo

Jesus resume a Lei no amor a Deus e ao próximo. Amar o vizinho como a si mesmo é cumprir toda a Lei.

Na biyun ita ce, Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ba wata doka da ta fi waɗannan."

Dukan doka an taƙaita a cikin umarni ɗaya ne cewa, "Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka."

Umarnan nan, "Kada ka yi zina." "Kada ka yi kisankai." "Kada ka yi sata." "Kada kuma ka yi ƙyashi." Da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma "Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka."

Ƙauna ba ta cutar da maƙwabci. Saboda haka ƙauna cika Doka ce.

Saboda haka, duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Doka da koyarwar Annabawa sun ƙunsa.

Amor em ação

O amor verdadeiro se mostra em ações concretas: hospitalidade, generosidade e cuidado com os necessitados ao nosso redor.

Gargaɗin ƙarshe

Ku ci gaba da ƙaunar juna kamar yan’uwa. Kada ku manta da yin alheri ga baƙi, gama ta yin haka ne waɗansu suka yi wa mala’iku hidima, ba da saninsu ba.

Addinin da Allah Ubanmu ya yarda da shi a matsayin mai tsabta da kuma marar aibi shi ne, a kula da marayu da gwauraye cikin damuwoyinsu, a kuma kiyaye kai daga lalacin da duniya take sa wa.

Fiye da kome, ku ƙaunaci juna sosai, domin ƙauna tana rufe zunubai masu ɗumbun yawa.

Saboda haka, in da hali, bari mu aikata nagarta ga dukan mutane, musamman ga waɗanda suke na iyalin masu bi.

Ku ƙaunaci juna

Wannan shi ne saƙon da kuka ji tun farko. Ya kamata mu ƙaunaci juna.

"Sabon umarni nake ba ku. Ku ƙaunaci juna. Kamar yadda na ƙaunace ku, ku ma ku ƙaunaci juna.

Edificação e encorajamento mútuo

Somos chamados a encorajar uns aos outros, carregar os fardos alheios e buscar o bem do próximo acima do próprio interesse.

Saboda haka ku ƙarfafa juna ku kuma gina juna, kamar dai yadda kuke yi.

Ku ɗauki nawayar juna, a haka kuwa za ku cika dokar Kiristi.

Ya kamata kowannenmu faranta wa maƙwabcinsa rai don kyautata zamansa domin kuma gina shi.

Kada wani kula da kansa kawai, sai dai kula da waɗansu kuma.

Ku ba da kanku ga juna cikin ƙauna irin ta yan’uwa. Kowa yi ƙoƙari wajen girmama wani fiye da kansa.

Ubangiji sa ƙaunarku ta ƙaru ta kuma yalwata ga juna da kuma ga kowa, kamar yadda tamu take muku.

Humildade, perdão e convivência

O relacionamento com o próximo exige humildade, paciência e disposição para perdoar. Não devemos julgar, mas acolher com compaixão.

Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai cikin tawali’u, ku ɗauki waɗansu sun fi ku.

Ku riƙa yin haƙuri da juna kuna kuma gafarta wa juna duk wani laifin da wani ya yi muku. Ku gafarta kamar yadda Ubangiji ya gafarce ku.

Saboda haka bari mu daina ba wa juna laifi. A maimakon, sai kowa yi niyya ba zai sa dutsen tuntuɓe ko abin sa fāɗuwa a hanyar ɗan’uwansa ba.

Shari’ar adalcin Allah

Saboda haka, kai da kake ba wa wani laifi, ba ka da wata hujja, gama a duk lokacin da kake ba wa wani laifi, kana hukunta kanka ne, domin kai da kake ba wa wani laifi kai ma kana aikata waɗannan abubuwa.

Shan wahala saboda yin ayyuka alheri

A ƙarshe, dukanku ku zauna lafiya da juna; ku zama masu juyayi, kuna ƙaunar juna kamar yan’uwa, ku zama masu tausayi da kuma tawali’u.

Wani yakan ɗauki wata rana da daraja fiye da sauran ranaku; wani kuma yana ganin dukan ranakun ɗaya ne. Ya kamata kowa kasance da tabbaci a cikin zuciyarsa.

"Duk wanda ya ƙi yi alheri ga aboki

ya rabu ta tsoron Maɗaukaki.

Seja o primeiro