Pular para o conteúdo
Publicidade

1 Tarihi 29:11,12,14,15

11 Girma da iko

da ɗaukaka, da daraja da kuma nasara naka ne, ya Ubangiji,

gama kome a sama da ƙasa naka ne.

Mulki kuma naka ne, ya Ubangiji;

an kuma ɗaukaka ka a matsayin kai a bisa duka.

12 Wadata da girma daga gare ka suke;

kai ne mai mulkin dukan abubuwa.

A hannuwanka ne ƙarfi da iko suke

don ka ɗaukaka da kuma ba da ƙarfi ga duka.

14 "Amma wane ni, kuma wace ce jama’ata da za mu iya ba ka a yalwace kamar haka? Kome daga gare ka suka fito, kuma mun ba ka abin da kawai ya fito daga hannunka ne. 15 Mu bare ne kuma baƙi a gabanka, kamar yadda dukan kakanninmu suke. Kwanakinmu a duniya suna kamar inuwa ne, ba sa zuciya.

Estes versículos te tocaram? Ore agora!

+581 estão orando agora.

Junte-se à corrente de oração.