15 Duk wanda ya yarda cewa Yesu Ɗan Allah ne, Allah yana raye a cikinsa, shi kuma a cikin Allah. 16 Ta haka muka sani, muke kuma dogara ga ƙaunar da Allah yake mana.
Allah ƙauna ne. Duk wanda yake rayuwa cikin ƙauna, yana rayuwa a cikin Allah ne, Allah kuma a cikinsa.