Pular para o conteúdo
Publicidade

1 Reis 19

20 Sai Elisha ya bar shanun, ya ruga ya bi Iliya. Ya ce, "Bari in sumbace mahaifina da mahaifiyata, in yi musu bankwana, sa’an nan in zo in bi ka."

Iliya ya ce, "Koma! Me na yi maka?"

21 Sai Elisha ya bar shi, ya koma, ya ɗauki shanunsa ya yayyanka. Ya ƙone kayan garman noman don dafa naman, ya kuma ba wa mutane naman, suka kuwa ci. Sa’an nan ya tashi, ya bi Iliya, ya kuma zama mai hidimarsa.

Veja também