Publicidade

1 Reis 3

5 A Gibeyon, Ubangiji ya bayyana ga Solomon da dare a mafarki, Allah ya ce, "Ka roƙi abin da kake so in ba ka."

6 Solomon ya amsa ya ce, "Ka nuna alheri mai girma ga bawanka, mahaifina Dawuda domin ya yi aminci gare ka da adalci, ya kuma kasance da zuciya mai gaskiya. Ka ci gaba da wannan alheri mai girma gare shi, ka ba shi ɗa don zauna a kujerar sarautarsa a wannan rana.

7 "Yanzu, ya Ubangiji Allahna, ka sa bawanka a wurin mahaifina Dawuda. Amma ni ɗan yaro ne kawai, ban kuma san yadda zan yi ayyukana ba. 8 Bawanka yana nan a cikin mutanen da ka zaɓa, mutane masu girma, waɗanda suka wuce ƙirge, ko a lissafta. 9 Saboda haka ka ba bawanka zuciyar ganewa, don shugabanci mutanenka, kuma iya rarrabe tsakanin abin da yake daidai da abin da ba daidai ba. Gama wa zai iya shugabance wannan mutanenka masu girma haka?"

10 Sai Ubangiji ya ji daɗi cewa Solomon ya roƙa wannan. 11 Saboda haka Allah ya ce masa, "Da yake ka nemi wannan ne, ba ka kuwa nemi tsawon rai ko arziki wa kanka ba, ba ka kuma nemi mutuwar abokan gābanka ba, amma ka nemi ganewa a aikata gaskiya, 12 zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-