An kawo akwatin alkawari a haikali
1 Sai Sarki Solomon ya tattara dattawan Urushalima a gabansa, da dukan shugabannin kabilu, da shugabannin iyalan Isra’ilawa, domin su kawo akwatin alkawarin Ubangiji daga Sihiyona, Birnin Dawuda. 2 Dukan mutanen Isra’ila suka tattaru a gaban Sarki Solomon a lokacin biki, a watan Etanim, wato, wata na bakwai.
3 Sa’ad da dukan dattawan Isra’ila suka iso, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin, 4 suka haura da akwatin alkawarin Ubangiji da kuma Tentin Sujada, da dukan kayayyaki masu tsarkin da suke cikinsa. Firistoci da Lawiyawa suka ɗauko su, 5 sai Sarki Solomon da dukan taron Isra’ila da suka tattaru kewaye da shi a gaban akwatin alkawari, suka yi ta miƙa hadayar tumaki da bijimai masu yawa da ba a iya lissaftawa, ko ƙirgawa.
6 Sa’an nan firistoci suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji inda aka shirya masa, can ciki cikin haikali, a Wuri Mafi Tsarki, aka kuma sa shi a ƙarƙashin fikafikan kerubobin. 7 Kerubobin sun buɗe fikafikansu a bisa wurin da akwatin alkawarin yake, suka inuwartar da akwatin alkawarin da sandunan ɗaukansa. 8 Waɗannan sandunan sun yi tsawo har ana iya ganin bakinsu daga Wuri Mai Tsarki a gaban wuri mai tsarki na can ciki, amma ba a iya ganinsu daga waje na Wuri Mai Tsarki ba. Suna nan kuwa a can har wa yau. 9 Ba kome a cikin akwatin alkawarin, sai dai alluna na dutse guda biyu waɗanda Musa ya ajiye a ciki tun a Horeb, inda Ubangiji ya yi alkawari da Isra’ilawa bayan sun fito Masar.
10 Sa’ad da firistoci suka janye daga Wuri Mai Tsarki, sai girgije ya cika haikalin Ubangiji. 11 Firistocin kuwa ba su iya yin hidimarsu ba saboda girgijen, gama ɗaukakar Ubangiji ta cika haikalinsa.