15 Sa’ad da bawan mutumin Allah ya farka ya kuma fita kashegari da sassafe, sai ga mayaƙa tare da dawakai da kekunan yaƙi sun kewaye birni. Sai bawan ya ce, "Ranka yă daɗe! Me za mu yi?"
16 Sai annabin ya ce, "Kada ka ji tsoro, waɗanda suke tare da mu sun fi waɗanda suke tare da su."
17 Sa’an nan Elisha ya yi addu’a ya ce, "Ya Ubangiji, ka buɗe idanunsa yă gani!" Sai Ubangiji ya buɗe idanun bawan, ya duba, ya ga tuddai cike da dawakai da keken yaƙin wuta kewaye da Elisha.