Pular para o conteúdo
Publicidade

Colossenses 1

12 kuna gode wa Uba, wanda ya sa kuka cancanci ku sami rabo a gādon tsarkaka a cikin mulkin haske. 13 Gama ya riga ya cece mu daga mulkin duhu ya kuma kawo mu cikin mulkin Ɗan da yake ƙauna, 14 wanda ta wurinsa muka sami fansa da kuma gafarar zunubai.

Fifikon Kiristi

15 Kiristi shi ne surar da ake gani na Allah wanda ba a iya gani, ɗan fari a kan dukan halitta. 16 Ta wurinsa aka halicci dukan abu, abubuwan da suke cikin sama da abubuwan da suke a duniya, waɗanda ake gani, da waɗanda ba a gani, ko kursiyoyi ko ikoki ko masu mulki ko hukumomi; an halicci dukan abu ta wurinsa da kuma dominsa ne. 17 Ya kasance kafin dukan abu, kuma a cikinsa ne dukan abubuwa suke a harhaɗe.

Veja também

Colossenses
Ver todos os capítulos de Colossenses