Publicidade

Eclesiastes 12

1 Ka tuna da Mahaliccinka

a kwanakin ƙuruciyarka,

kafin lokacin wahala ta zo

shekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce,

"Ba na jin daɗinsu,"

2 kafin rana da haske

wata da taurari su daina haske,

gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;

3 sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki,

majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi,

sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa,

idanun da suke duba ta taga suka duhunta;

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-