14 Gama shi kansa shi ne salamarmu, shi ne ya kawo ƙungiyoyi biyu suka zama ɗaya, ya kuma rushe katangan nan ta ƙiyayya wadda ta raba mu. 15 Kiristi ya ba da jikinsa don yă kawar da doka da dukan umarnanta da kuma ƙa’idodinta. Ya yi haka domin yă halicci sabuwar zuriya daga zuriyoyin nan biyu. Ta haka kuma ya kawo salama tsakaninsu.
Publicidade
Publicidade