10 Sa’an nan ɗayansu ya ce, "Lalle zan komo wurinka war haka shekara mai zuwa. Saratu matarka kuwa za tă haifi ɗa."
Saratu kuwa tana a bayansu tana ji daga mashigin tenti. 11 Ibrahim da Saratu dai sun riga sun tsufa sosai. Saratu kuma ta wuce shekarun haihuwa. 12 Saboda haka Saratu ta yi dariya da ta yi tunani a zuci tana cewa, "Bayan ƙarfina ya ƙare, maigidana18.12 Ko kuwa miji kuma ya tsufa, yanzu zan sami wannan jin daɗi?"