Pular para o conteúdo
Publicidade

Farawa 2

18 Ubangiji Allah ya ce, "Bai yi kyau mutumin kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi."

19 To, Ubangiji Allah ya yi dukan namun jeji da dukan tsuntsayen sama daga ƙasa. Ya kawo su wurin mutumin don ga wanda suna zai kira su; kuma duk sunan da mutumin ya kira kowane mai rai, sunansa ke nan. 20 Saboda haka mutumin ya sa wa dukan dabbobi, da tsuntsayen sama da dukan namun jeji sunaye.

Amma ba a sami mataimakin da ya dace da Adamu ba. 21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

23 Sai mutumin ya ce,

"Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

nama kuma na namana.

Za a ce da ita mace,

gama an ciro ta daga namiji."

24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Veja também