Pular para o conteúdo
Publicidade

Gênesis 2

21 Saboda haka Ubangiji Allah ya sa mutumin ya yi barci mai nauyi; yayinda yake barci sai ya ɗauko ɗaya daga cikin haƙarƙarin mutumin, ya kuma rufe wurin da nama. 22 Sa’an nan Ubangiji Allah ya yi mace daga haƙarƙarin da ya ɗauko daga mutumin, ya kuwa kawo ta wurin mutumin.

23 Sai mutumin ya ce,

"Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana

nama kuma na namana.

Za a ce da ita mace,

gama an ciro ta daga namiji."

24 Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.

Veja também