17 Ga Adamu kuwa ya ce, "Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’
"Za a la’anta ƙasa saboda kai.
Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
18 Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya
za ka kuwa ci ganyayen gona.
19 Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,
da yake daga cikinta aka yi ka.
Gama kai turɓaya ne,
kuma ga turɓaya za ka koma."