Pular para o conteúdo
Publicidade

Gênesis 6

Mugunta a duniya

1 Sa’ad da mutane suka fara ƙaruwa a duniya, aka kuma hahhaifi musu ya’ya mata, 2 sai ya’yan Allah maza suka ga cewa ya’yan mutane mata suna da bansha’awa, sai suka zaɓi waɗanda suke so, suka aura. 3 Sa’an nan Ubangiji ya ce, "Ruhuna ba zai zauna a cikin mutum har abada ba, saboda shi mai mutuwa ne, kwanakinsa za su zama shekaru ɗari da arba’in ne."

4 Nefilimawa suna nan a duniya a waɗancan kwanaki, da kuma kwanakin da suka bi baya, a sa’ad da ya’yan Allah suka kwana da ya’yan mutane mata, suka kuma hahhaifi musu ya’ya. Ai, su ne jarumawan , mutanen da suka shahara.

5 Ubangiji kuwa ya lura cewa muguntar mutum ta yi yawa a duniya, kuma kowane abin da yake tunani a zuciyarsa mugu ne kawai a kowanne lokaci. 6 Ubangiji ya damu da ya yi mutum a duniya, abin ya zafe shi ƙwarai. 7 Saboda haka Ubangiji ya ce, "Zan kawar da mutum, da dabbobi, da halittu masu rarrafe a ƙasa da kuma tsuntsayen sama waɗanda na halitta, daga doron ƙasa, saboda na damu da na yi su." 8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a gaban Ubangiji.

9 Ga tarihin Nuhu.

Nuhu mutum ne mai adalci, marar abin zargi a cikin mutanen zamaninsa, ya kuma yi tafiya tare da Allah.

Veja também