13 Saboda haka, Allah ya ce wa Nuhu, "Zan kawo ƙarshen dukan mutane, gama saboda su duniya ta cika da tashin hankali. Lalle zan hallaka su da kuma duniya. 14 Saboda haka ka yi wa kanka jirgi da katakon Saifires6.14 Babu tabbas game da ma’anar kalman nan a Ibraniyanci., ka yi ɗakuna a cikinsa, ka shafe shi da ƙaro ciki da waje. 15 Ga yadda za ka gina shi; jirgin zai kasance mai tsawon ƙafa 45, fāɗinsa ƙafa 75, tsayinsa kuma ƙafa 45. 16 Ka yi masa rufi, ka kuma ba da fili inci 18 tsakanin rufin a kowane gefen jirgin.6.16 Ko kuwa Ka bar inda haske zai shiga ta wurin gamawa Ka sa ƙofa a gefen jirgin. Ka yi shi hawa uku, ka yi ƙofa a gefe.
Publicidade