Pular para o conteúdo
Publicidade

Hebreus 9

Sujada a cikin tabanakul na duniya

1 Alkawarin farko ya ƙunshi ƙa’idodi don sujada da kuma tsattsarkan wuri a duniya. 2 An kafa tabanakul. A cikin ɗakinsa na farko akwai wurin ajiye fitila, tebur da kuma keɓaɓɓen burodi; an kira wannan Wuri Mai Tsarki. 3 Sa’an nan akwai labule, kuma a bayan labulen akwai ɗaki na biyu da ake kira Wuri Mafi Tsarki, 4 wanda yake da bagaden zinariya na turare da kuma akwatin alkawarin da aka dalaye da zinariya. A cikin akwatin alkawarin akwai tulun zinariya mai Manna a ciki, sandan Haruna wanda ya yi toho, da kuma allunan dutsen alkawari. 5 A bisa akwatin alkawarin kuwa akwai kerubobi na Ɗaukaka, waɗanda suka inuwantar da murfin kafara da fikafikansu.9.5 A al’adance mazaunin jinƙai Sai dai ba za mu tattauna waɗannan abubuwa dalla-dalla a yanzu ba.

Veja também