Yesu da kamun kifin banmamaki
1 Daga baya Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiransa, a bakin Tekun Tibariya.21.1 Wato, Tekun Galili Ga yadda ya faru. 2 Siman Bitrus, Toma (wanda ake kira Didaimus), Natanayel daga Kana ta Galili, ’ya’yan Zebedi maza, da kuma waɗansu almajirai guda biyu suna tare. 3 Sai Siman Bitrus ya ce musu, "Za ni kamun kifi," suka ce, "Za mu tafi tare da kai." Saboda haka suka fita suka shiga jirgin ruwa, amma a daren nan ba su kama kome ba.
4 Da sassafe, sai ga Yesu tsaye a gaci, amma almajiran ba su gane cewa Yesu ne ba.
5 Sai ya ce musu, "Abokai, kuna da kifi kuwa?"
Suka amsa suka ce, "A’a."
6 Ya ce musu, "Ku jefa abin kamun kifinku dama da jirgin ruwan, za ku samu." Da suka yi haka, sai suka kāsa jawo abin kamun kifin saboda yawan kifi.
7 Sai almajirin da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, "Ai, Ubangiji ne!" Nan da nan da Siman Bitrus ya ji ya ce, "Ai, Ubangiji ne," sai ya yafa mayafinsa (don dā ma ya tuɓe shi), ya fāɗa cikin ruwan. 8 Sauran almajiran kuwa suka bi shi cikin jirgin ruwan, janye da abin kamun kifin cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, wajen yadi ɗari ne. 9 Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.
10 Yesu ya ce musu, "Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu." 11 Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba.