Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 19

Zakka mai karɓar haraji

1 Yesu ya shiga Yeriko, yana ratsa ta cikinta. 2 Akwai wani mutum a garin, mai suna Zakka. Shi shugaban masu karɓar haraji ne, mai arziki kuma. 3 Ya so ga ko wane ne Yesu, amma saboda taron, bai iya ba, domin shi gajere ne. 4 Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.

5 Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, "Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau." 6 Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.

7 Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, "Ya je don zama baƙon mai zunubi.’ "

8 Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, "Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu."

9 Sai Yesu ya ce masa, "Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne. 10 Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin nemi abin da ya ɓata, cece shi kuma."

Veja também