Pular para o conteúdo
Publicidade

Lucas 8

43 A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. 44 Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.

45 Yesu ya yi tambaya, "Wa ya taɓa ni?"

Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, "Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe."

46 Amma Yesu ya ce, "Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina."

47 Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take. 48 Sai Yesu ya ce mata, "Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya."

Veja também