15 Ashe, Ubangiji bai maishe su ɗaya ba? Cikin jiki da ruhu, su nasa ne. Me ya sa suke ɗaya? Domin yana neman ’ya’ya masu tsoron Allah.2.15 Ko kuwa 15 Amma wanda yake mahaifinmu bai yi haka ba, muddin yana da rai. Me yake nema? Zuriya daga Allah Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amanar matar ƙuruciyarka.
16 "Na ƙi kisan aure," in ji Ubangiji, Allah na Isra’ila. "Na kuma ƙi mutumin da ya rufe kansa da tashin hankali kamar riga," in ji Ubangiji Maɗaukaki.
Saboda haka sai ka lura da kanka, kada kuma ka ci amana.