Shaidar Bitrus a kan Kiristi
13 Sa’ad da Yesu ya zo yankin Kaisariya Filibbi, sai ya tambayi almajiransa ya ce, "Wa mutane suke ce da Ɗan Mutum?"
14 Suka amsa, "Waɗansu suna ce Yohanna Mai Baftisma; waɗansu kuma suna ce annabi Iliya; har wa yau waɗansu suna ce Irmiya ne ko kuma ɗaya daga cikin annabawa."
15 Ya tambaye su, "Amma ku fa, wane ne ni a ganinku?"
16 Siman Bitrus ya amsa ya ce, "Kai ne Kiristi,16.16 Ko kuwa a Almasihu; haka ma a aya 20 Ɗan Allah mai rai."