Publicidade

Oséias 10

1 Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa;

ya fitar da ya’ya wa kansa.

Yayinda ya’yan suka ƙaru,

ya gina ƙarin bagadai;

da ƙasarsa ta wadata,

ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.

2 Zuciyarsu masu ruɗu ne,

yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu.

Ubangiji zai rushe bagadansu

kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.

3 Sa’an nan za su ce, "Ba mu da sarki

domin ba mu girmama Ubangiji ba.

Amma ko da ma muna da sarki,

me zai yi mana?"

4 Sun yi alkawura masu yawa,

suka yi rantsuwar ƙarya

da kuma yarjejjeniyoyi;

saboda haka ƙararraki suka taso

kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.

5 Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro

saboda gunki maraƙin Bet-Awen.10.5 Bet-Awen yana nufin gidan mugunta (suna don Betel, wanda yake nufin gidan Allah).

Mutanensa za su yi makokinsa,

haka ma firistocinsa matsafa,

waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa,

don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.

6 Za a ɗauke shi a kai Assuriya

kamar gandu wa babban sarki.

Efraim zai sha kunya;

Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.

7 Samariya da sarkinta za su ɓace

kamar kumfa a bisa ruwaye.

8 Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta

zunubin Isra’ila ne.

Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma

su rufe bagadansu.

Sa’an nan za su ce wa duwatsu, "Ku rufe mu!"

Ga tuddai kuma, "Ku fāɗo a kanmu!"

9 "Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila,

a can kuwa kuka ci gaba.10.9 Ko kuwa a can aka ɗauki matsayi

Yaƙi bai cimma

masu aikata mugunta a Gibeya ba?

10 Sa’ad da na ga dama, zan hukunta su;

al’ummai za su taru su yi gāba da su

don su daure su saboda zunubansu da suka riɓanya.

11 Efraim horarriyar karsana ce

mai son sussuka;

saboda haka zan sa karkiya

a kyakkyawan wuyanta.

Zan bi da Efraim,

Dole Yahuda yi noma,

dole kuma Yaƙub ja garman noma.

12 Ku shuka wa kanku adalci,

ku girbe ya’yan jinƙai marar ƙarewa,

ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba;

gama lokaci ne na neman Ubangiji,

sai ya zo

ya zubo adalci a kanku.

13 Amma kun shuka mugunta,

kuka girbe mugu

kuka ci ya’yan ruɗu.

Domin kun dogara da ƙarfinku

da kuma a jarumawanku masu yawa,

14 hayaniyar yaƙi za tashi gāba da mutanenku,

saboda a ragargaza kagaranku,

kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi,

sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da ya’yansu da ƙasa.

15 Haka zai faru da kai, ya Betel,

domin muguntarka ta yi yawa.

Sa’ad da wannan rana ta zo,

za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf.

Veja também

Bíblia Online Bíblia Online

Bíblia Online • Versão: 2026-07-05_19-25-13-