14 Babbar ranar Ubangiji ta yi kusa,
ta yi kusa kuma tana zuwa da sauri.
Ku saurara! Kukan ranar Ubangiji za tă yi zafi,
za a ji kururuwan jarumi a can.
15 Ranan nan za tă zama ranar fushi,
rana ce ta baƙin ciki da azaba,
rana ce ta tashin hankali da lalacewa,
ranar duhu baƙi ƙirin,
ranar gizagizai da baƙin duhu,
16 rana ce ta busa ƙaho da kururuwar yaƙi
gāba da birane masu mafaka,
da kuma kusurwar hasumiyoyi.
17 "Zan kawo baƙin ciki a kan mutane
za su kuma yi tafiya kamar makafi,
domin sun yi wa Ubangiji zunubi.
Za a zubar da jininsu kamar ƙura
kayan cikinsu kuma kamar najasa.
18 Azurfarsu ko zinariyarsu
ba za su iya cetonsu ba
a ranar fushin Ubangiji."
A cikin zafin kishinsa
za a hallaka dukan duniya
gama zai kawo ƙarshen dukan mazaunan duniya
nan da nan.