Pular para o conteúdo
Publicidade

Agradecimento pela família

Por Bíblia Online

Agradecer pela família é reconhecer a bênção mais preciosa que Deus nos concede. Os filhos são herança do Senhor — cada membro da família é presente divino a ser celebrado.

Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji,

yara lada ne daga gare shi.

Kamar kibiyoyi a hannun jarumi

haka ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.

Mai albarka ne mutumin

da korinsa sun cika da su.

Ba za a kunyata su ba

sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

Yabi Ubangiji, ya raina;

dukan abin da yake cikin cikina, yabi sunansa mai tsarki.

Yabi Ubangiji, ya raina,

kada kuma ka manta dukan alheransa,

Ba za mu ɓoye su wa ya’yanmu ba;

za mu faɗa wa tsara mai zuwa

ayyukan da suka zama yabo na Ubangiji,

ikonsa, da abubuwan banmamakin da ya aikata.

Jikoki rawanin tsofaffi ne,

kuma iyaye su ne abin taƙamar ya’yansu.

Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi.

Godiya da addu’a

Ina gode wa Allahna a kowane lokacin da na tuna da ku.

Wace irin godiya ce za mu yi wa Allah saboda ku a kan dukan farin cikin da muke da shi a gaban Allahnmu ta dalilinku?

Ku yabi Ubangiji, ku iyalan al’ummai,

ku yabi ɗaukaka da ƙarfin Ubangiji,

Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.

Daga yalwar alherinsa dukanmu muka sami albarka bisa albarka.

Mata suka ce wa Na’omi, "Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda a wannan rana bai bar ki ba tare da dangi mai fansa ba. Allah sa zama sananne a dukan Isra’ila! Zai sabunta rayuwarki adana ki a tsufanki. Gama surukarki wadda take ƙaunarki wadda kuma take mafi kyau gare ki fiye da ya’ya maza bakwai, ta haife shi."

Masu rai, masu rai, su suke yabonka,

kamar yadda nake yi a yau;

iyaye za su faɗa wa ya’yansu

game da amincinka.

Seja o primeiro