Criação
A criação revela a glória de Deus. Céus, terra, mares e tudo o que existe testemunham o poder criador. No princípio Deus criou — e tudo era muito bom.
No princípio
No princípio criou Deus os céus e a terra. O Espírito de Deus pairava sobre as águas. E Deus disse: haja luz.
A farko-farko, Allah ya halicci sama da ƙasa. To, ƙasa dai ba ta da siffa, babu kuma kome a cikinta, duhu ne kawai ya rufe ko’ina, Ruhun Allah kuwa yana yawo a kan ruwan.
Sa’an nan Allah ya ce, "Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa."
Saboda haka Allah ya halicci mutum cikin siffarsa.
Cikin kamannin Allah, Allah ya halicci mutum.
Miji da mace ya halicce su.
Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
Ubangiji Allah ya ce, "Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi."
O poder criador
Pela palavra do Senhor foram feitos os céus. Tudo foi criado por Ele e para Ele — o visível e o invisível.
Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai,
rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
Kafin a haifi duwatsu
ko a fid da ƙasa da duniya,
daga madawwami zuwa madawwami kai Allah ne.
Ku zo, bari mu rusuna mu yi sujada,
bari mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu;
Na tā da idanuna zuwa wajen tuddai,
ta ina ne taimakona zai zo?
Taimakona zai zo daga wurin Ubangiji,
wanda ya kafa sama da ƙasa.
Taimakonmu yana a sunan Ubangiji,
Wanda ya yi sama da ƙasa.
Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya yi;
bari mu yi farin ciki mu kuma yi murna a cikinta.
Gama ka halicci ciki-cikina;
ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki;
ayyukanka suna da banmamaki,
na san da haka sosai.
Criador e Sustentador
O Deus eterno não se cansa nem se fatiga. Dele, por Ele e para Ele são todas as coisas — a Ele seja a glória.
Ba ku sani ba?
Ba ku ji ba?
Ubangiji madawwamin Allah ne,
Mahaliccin iyakokin duniya.
Ba zai taɓa gaji ko yă kasala ba,
kuma fahimtarsa ya wuce gaban ganewar mutum.
"Kaitonka mai gardama da Wanda ya yi ka,
da wanda yake kasko a cikin kasko a ƙasa.
Yumɓu ya iya ce wa magini,
‘Me kake yi?’
Aikinka na iya cewa,
‘Ba shi da hannuwa’?
"A, Ubangiji Mai Iko Duka, ka yi sammai da duniya ta wurin ikonka mai girma da kuma hannunka mai iko. Ba abin da ya gagare ka.
shi da ya gina kyakkyawar fadarsa a cikin sammai
ya kuma kafa harsashenta a duniya,
shi da yakan kira ruwan teku
yă kuma kwarara su a bisa duniya,
Ubangiji ne sunansa.
Gama daga gare shi, ta wurinsa, da kuma saboda shi ne dukan abubuwa suka kasance.
Ɗaukaka ta tabbata a gare shi har abada! Amin.
Gama tun halittar duniya halayen Allah marar ganuwa, madawwamin ikonsa da kuma allahntakarsa, ana iya ganinsu sarai, ana fahimtarsu ta wurin abubuwan da Allah ya halitta, domin kada mutane su sami wata hujja.
Halitta tana jira da marmari ta ƙosa ta ga bayyanuwar ’ya’yan Allah.
Nova criação
Se alguém está em Cristo, nova criatura é. O Criador faz novas todas as coisas — na natureza e na redenção.
Saboda haka, duk wanda yake cikin Kiristi, sabuwar halitta ce, tsohon al’amari ya shuɗe, sabon ya zo!
Ai, mu aikinsa ne, an sāke halittarmu a cikin Kiristi Yesu musamman domin mu yi kyawawan ayyuka, waɗanda Allah ya tanadar mana tun da fari, mu yi.
Ya zaɓa yă haife mu ta wurin kalmar gaskiya, domin mu zama ’ya’yan fari na dukan abin da ya halitta.
Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne.
‘Gama a cikinsa ne muke rayuwa muke motsi muka kuma kasance.’ Yadda waɗansu mawaƙanku suka ce, ‘Mu zuriyarsa ce.’
Sa’an nan na ji kowace halitta a sama da ƙasa da ƙarƙashin ƙasa da kuma bisan teku, da kome da yake cikinsu yana rerawa,
"Gare shi mai zama a kan kursiyin da kuma ga Ɗan Ragon
yabo da girma da ɗaukaka da iko,
sun tabbata har abada abadin!"