Frutos do Espírito
Os frutos do Espírito são evidências visíveis da presença de Deus na vida do crente. Amor, alegria, paz, paciência — são marcas que diferenciam os filhos de Deus no mundo.
O fruto do Espírito
O fruto do Espírito é amor, alegria, paz, paciência, amabilidade, bondade, fidelidade, mansidão e domínio próprio. Contra estas coisas não há lei.
Amma amfanin da Ruhu yake bayar shi ne ƙauna, farin ciki, salama, haƙuri, kirki, nagarta, aminci, sauƙinkai, da kuma kamunkai. Ai, ba ruwan Doka da waɗannan abubuwa.
Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ’ya’yan haske (domin amfanin haske ya ƙunshi nagarta, adalci, da kuma gaskiya) ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji.
Amma hikimar da ta zo daga sama da fari tana da tsabta gaba ɗaya; sa’an nan mai ƙaunar salama ce, mai sanin ya kamata, mai biyayya, cike da jinƙai da aiki mai kyau, marar nuna bambanci, sahihiya kuma. Masu salama da suke shuki cikin salama sukan girbe adalci.
Saboda haka ’yan’uwana, ku ma kun mutu ga dokar ta wurin jikin Kiristi, domin ku zama na wani, gare shi wanda aka tashe shi daga matattu, don mu ba da amfani ga Allah. Gama sa’ad da halin mutuntaka yake mulkinmu, sha’awace-sha’awacen zunubi waɗanda dokar ta zuga sun yi ta aiki a jikunanmu, don mu ba da amfani wa mutuwa. Amma yanzu, ta wurin mutuwa ga abin da dā ya daure mu, an sake mu daga dokar saboda mu yi hidima a sabuwar hanyar Ruhu, ba a tsohuwar hanyar rubutaccen ƙa’ida ba.
Wace riba ce kuka samu a lokacin, daga abubuwan nan da yanzu suka zama muku abin kunya? Ƙarshen irin abubuwan nan dai, mutuwa ne! Amma a yanzu da aka ’yantar da ku daga zunubi kuka kuma zama bayi ga Allah, ribar da kuka samu tana kai ga zaman tsarki, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.
Permanecer em Cristo
Quem permanece em Cristo dá muito fruto. Toda árvore boa produz bons frutos — e é pelo fruto que se conhece a árvore.
Ku kasance a cikina, ni kuma zan kasance a cikinku. Babu reshen da zai iya yin ’ya’ya da kansa, dole yă kasance a jikin kuringar inabin. Haka ku ma, ba za ku iya ba da ’ya’ya ba sai kun kasance a cikina.
"Ni ne kuringar inabin; ku ne kuma rassan. In mutum ya kasance a cikina ni kuma a cikinsa, zai ba da ’ya’ya da yawa; in ba tare da ni ba, ba za ku iya yin kome ba.
Wannan ne yakan kawo ɗaukaka ga Ubana, ku ba da ’ya’ya da yawa, kuna kuma nuna kanku ku almajiraina ne.
"Ba itace mai kyau da yake ba da munanan ’ya’ya. Mummunan itace kuma ba ya ba da ’ya’ya masu kyau. Kowane itace da irin ’ya’yansa ne ake saninsa. Mutane ba sa tsinke ’ya’yan ɓaure daga ƙaya, ko kuwa ’ya’yan inabi daga sarƙaƙƙiya. Mutumin nagari yakan nuna abubuwa nagari daga cikin nagarta da yake a ɓoye a zuciyarsa, mugun mutum kuwa yakan nuna mugayen abubuwa daga muguntar da take a ɓoye a zuciyarsa. Gama baki yakan faɗa abin da ya cika zuciya ne."
Ku yi ayyukan da suka dace da tuba.
Semear e colher
Quem semeia na justiça colherá fruto de vida. Os frutos do Espírito são a colheita de uma vida plantada no Senhor.
Ku shuka wa kanku adalci,
ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa,
ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba;
gama lokaci ne na neman Ubangiji,
sai ya zo
ya zubo adalci a kanku.
Ku faɗa wa masu adalci cewa kome zai zama musu da kyau,
gama za su ji daɗin aikin da hannuwansu suka yi.
Ba haka kaɗai ba ma, mu kanmu da muke da nunan fari na Ruhu, muna nishi a ciki-cikinmu yayinda muke jira da marmari a maishe mu ’ya’yan riƙo na Allah, fansar jikunanmu.
’Ya’yan itacena sun fi zinariya zalla;
amfanin gonar da nake bayar ya fi azurfa mafi kyau.