34 Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne;
ƙaunarsa madawwamiya ce.
35 Ku yi kuka, ku ce, "Cece mu, ya Allah Mai Cetonmu;
tara mu ka kuma cece mu daga al’ummai,
don mu yi godiya ga sunanka mai tsarki,
don mu ɗaukaka a cikin yabonka."
36 Yabi Ubangiji, Allah na Isra’ila,
daga madawwami zuwa madawwami.
Sai dukan mutane suka ce, "Amin." Suka kuma "Yabi Ubangiji."