20 Amma mu ’yan mulkin sama ne. Muna kuma jira zuwan Mai Ceto daga can, Ubangiji Yesu Kiristi, 21 shi ne mai ikon kawo dukan abubuwa ƙarƙashin mulkinsa. Ta wurin ikon nan nasa zai sāke jikin nan namu na ƙasƙanci, yă mai da shi kamar jikin nan nasa na ɗaukaka.