7 Nuhu da matarsa da ’ya’yansa da matansu, suka shiga jirgi domin su tsira daga ruwa ambaliya. 8 Biyu-biyu daga dabbobi masu tsabta da marasa tsabta, da tsuntsaye da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa, 9 namiji da ta mace, suka zo wurin Nuhu, suka shiga jirgi, kamar yadda Allah ya umarce Nuhu. 10 Bayan kwana bakwai kuwa ambaliya ruwa ta sauko a bisa duniya.
Publicidade