4 "Kana ina lokacin da na aza harsashen duniya?
Gaya mini, in ka sani.
5 Wane ne ya zāna girmanta? Ba shakka ka sani!
Wane ne ya ja layin aunawa a kanta?
6 A kan me aka kafa tushenta,
ko kuma wa ya sa dutsen kan kusurwarta,
7 yayinda taurarin safe suke waƙa tare
dukan mala’iku kuma suka yi sowa don farin ciki.
8 "Wane ne ya rufe teku a bayan ƙofofi,
lokacin da ya burtsatso daga cikin ciki.
9 Lokacin da na yi wa gizagizai riga
na kuma naɗe su a cikin duhu sosai,
10 sa’ad da na yi masa iyaka na
sa masa ƙofofi da wurin kullewa.
11 Sa’ad da na ce ga iyakar inda za ka kai,
ga inda raƙuman ruwanka za su tsaya?