Pular para o conteúdo
Publicidade

Hosiya 3

Sulhun Hosiya da matarsa

1 Ubangiji ya ce mini, "Ka tafi, ka sāke nuna wa matarka ƙauna, ko da yake wani yana son ta, ita kuma mazinaciya ce. Ka ƙaunace ta yadda Ubangiji yake ƙaunar Isra’ilawa, ko da yake sun juya ga waɗansu alloli suna kuma ƙauna wainar zabibi mai tsarki."

2 Ta haka na saye ta da shekel goma sha biyar na azurfa da kuma wajen buhu na sha’ir. 3 Sai na faɗa mata, "Za ki zauna tare3.3 Ko kuwa jira da ni kwanaki masu yawa; kada ki yi karuwanci ko ki yi abuta da wani namiji, ni kuwa zan zauna tare3.3 Ko kuwa jira da ke."

Veja também